Amfanin Tsofaffin Gwamnoni Ya Zo, Atiku, Obi Tinubu Sun Fara Shirin Kamfen Zaben 2027
- Jam'iyyun siyasa sun fara kammala shirye-shiryen yakin neman zaben 2027, an fara neman daraktocin yakin neman zabe
- ADC na duba yiwuwar nada tsohon gwamna a Sokoto a matsayin daraktan yakin neman zaben Atiku, yayin da APC ke nazarin wani daga Imo
- LP, SDP da sauran jam'iyyu sun ce za su bayyana cikakken tsarin yakin neman zabensu kafin ranar 19 ga Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yayin da ya rage kasa da makonni biyu a fara yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2027, an fara zawarcin daraktocin kamfe.
Manyan jam'iyyun siyasa sun kara zafafa tattaunawa kan wadanda za su jagoranci kwamitocin yakin neman zabensu.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin gwamnoni ne suka fi fitowa a matsayin manyan 'yan takarar mukamin daraktan yakin neman zabe, cewar Punch.
Wadanda za su iya sanin mukamin
Rahotanni sun nuna cewa APC na nazarin tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, da gwamnan Imo, Hope Uzodimma, domin jagorantar yakin neman sake zaben Shugaba Bola Tinubu.
A bangaren ADC kuwa, tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, ne ya fi samun karbuwa wajen zama daraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar.
Masu lura da harkokin siyasa sun ce mukamin daraktan yakin neman zabe na daga cikin mafi muhimmanci bayan dan takara da mataimakinsa.
A ADC, majiyoyi sun ce Aminu Waziri Tambuwal ne ke kan gaba wajen zama daraktan yakin neman zaben Atiku. Idan hakan ta tabbata, zai sake rike mukamin da ya taba yi a zaben 2023 lokacin da Atiku ya tsaya takara karkashin PDP.
Wata majiya ta kusa da Atiku ta tabbatar cewa Tambuwal ne ya fi samun amincewa a halin yanzu, cewar Daily Post.
Ta kuma bayyana cewa zai yi aiki tare da mataimakin Atiku, tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi, wajen tsara da aiwatar da dabarun yakin neman zabe a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na tsaka mai wuya, jam'iyyar PDP ta yi bayani
Ana kallon Tambuwal a matsayin gogaggen dan siyasa saboda ya taba zama kakakin majalisar wakilai, gwamnan Sokoto na wa'adi biyu, kuma yanzu sanata ne mai wakiltar Sokoto ta Kudu.

Source: Twitter
APC ta fara neman daraktan yakin kamfe
A bangaren APC kuwa, majiyoyi daga fadar shugaban kasa da jam'iyyar sun ce Hope Uzodimma da Tanko Al-Makura ne suka fi samun karbuwa wajen jagorantar yakin neman sake zaben Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.
Majiyoyin sun ce har yanzu ba a yanke hukunci na karshe ba, sai dai Hope Uzodimma na samun goyon bayan wasu manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar.
An ce yiwuwar zaben Uzodimma na da nasaba da kokarin APC na nuna daidaiton addini, kasancewar Tinubu da Shettima duk Musulmai ne, hakan na iya taimakawa wajen kara jawo hankalin masu zaben Kirista.
Hope Uzodimma na daga cikin amintattun abokan siyasar Shugaba Tinubu kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC.
Tanko Al-Makura ma na cikin jiga-jigan APC tun kafuwarta, kuma yana daga cikin wadanda suka taka rawa wajen hadewar jam'iyyun da suka kafa APC a shekarar 2013.
Atiku ya caccaki salon mulkin Tinubu
An ji cewa Atiku Abubakar ya ce babu wata farfaganda da za ta iya ɓoye tsananin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta.
Ya kalubalanci gwamnatin Bola Tinubu kan ci gaba da karɓo bashi duk da ikirarin ƙaruwa a kudaden shiga da cire tallafin mai.
Dan takarar shugaban ƙasar ya shaida wa gwamnati abin da ya kamata a mayar da hankali a kai ba batun kokarin kare sunanta a idon jama'a ba.
Asali: Legit.ng

