Musulmi Ya Sake Gumurzu a Siyasar Amurka, Abdul El Sayed Ya Lashe Zabe
- Abdul El-Sayed ya kayar da Haley Stevens a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar Democrats domin kujerar Sanatan Michigan
- Nasarar ta zo duk da cewa an kashe miliyoyin daloli wajen yaƙin neman zaɓe domin dakile shi da goyon bayan manyan jiga-jigan jam'iyyar
- El-Sayed zai fafata da tsohon ɗan majalisar wakilai Mike Rogers a babban zaɓen watan Nuwamba da ake sa ran zai kasance mai zafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Detroit, Michigan – Tsohon jami'in kula da lafiya, Abdul El-Sayed, ya samu nasarar lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Amurka na jam'iyyar Democrats a jihar Michigan.
El-Sayed ya doke 'yar majalisar wakilai, Haley Stevens, a zaɓen fitar da gwani, duk da gagarumin goyon baya da Stevens ta samu daga manyan shugabannin jam'iyyar da kuma kuɗin yaƙin neman zaɓe da suka kai kusan dala miliyan 65.

Source: Getty Images
NBC News ta bayyana cewa El-Sayed zai kara da tsohon ɗan majalisar wakilai, Mike Rogers, wanda ya zama ɗan takarar jam'iyyar Republican ba tare da hamayya ba.
Yadda El-Sayed ya samu nasara
Nasarar Abdul El-Sayed ta zo ne duk da cewa Gwamnar Michigan, Gretchen Whitmer, da Sanata Gary Peters sun mara wa Haley Stevens baya kafin zaɓen.
An kuma ɗauki zaɓen a matsayin gwajin ƙarfin masu ra'ayin sauyi na jam'iyyar Democrats a yankin Midwest, bayan irin nasarorin da suka samu a wasu jihohi.
El-Sayed ya yi kamfen ne kan batutuwan samar da inshorar lafiya ga kowa, rage tasirin kuɗi a siyasa da kuma suka ga tallafin da Amurka ke bai wa Isra'ila.
'Yan siyasa sun mara masa baya
Sanata Bernie Sanders da 'yar majalisar wakilai Alexandria Ocasio-Cortez sun yi kamfen tare da El-Sayed a Michigan.
Haka kuma ƙungiyar United Auto Workers (UAW), wacce ke da ƙarfi a jihar, ta bayyana goyon bayanta gare shi kamar yadda Al-Jazeera ta wallafa.

Kara karanta wannan
2027: Yadda Tinubu, Atiku da sauran ƴan takara ke shirin amfani da tsofaffin gwamnoni
A gefe guda, Haley Stevens ta samu goyon bayan manyan shugabannin Democrats da kuma ƙungiyoyin da suka kashe fiye da dala miliyan 30 wajen tallata ta.

Source: Getty Images
Zaɓen Nuwamba zai yi zafi
Ana sa ran zaɓen tsakanin Abdul El-Sayed da Mike Rogers zai kasance ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a Amurka, domin sakamakonsa na iya tasiri kan wacce jam'iyya za ta mallaki rinjaye a Majalisar Dattawa.
Jam'iyyar Republican na da kujeru 53 a majalisar, yayin da Democrats ke ƙoƙarin ƙwace ƙarin kujeru domin samun rinjaye.
El-Sayed zai gaji kujerar Sanata Gary Peters, wanda ya sanar da cewa ba zai sake neman wa'adi na uku ba.
Rashida ta lashe zabe a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilan Amurka, Rashida Tlaib, ta sake lashe tikitin jam'iyyar Democrats domin wakiltar mazabar Michigan ta 12.
Tlaib ta kayar da abokan hamayyarta Shanelle Jackson da Byron Nolen cikin gagarumar nasara bayan samun fiye da 64% na ƙuri'un da aka ƙidaya.
Nasarar tata ta ƙara nuna irin ƙarfin masu ra'ayin sauyi a cikin jam'iyyar Democrats gabanin babban zaɓen watan Nuwamban shekarar 2026.
Asali: Legit.ng
