Mai Neman Takarar Gwamna a Gombe Ya Saba da Pantami, Ya Goyi bayan Zabin APC

Mai Neman Takarar Gwamna a Gombe Ya Saba da Pantami, Ya Goyi bayan Zabin APC

  • Daya daga cin masu neman tikitin APC din tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2027, Hon. Usman Bello Kumo, ya amince da matsayar da jam'iyyar ta cimma
  • Babban mai tsawatarwar a majalisar wakilai ya bayyana cewa ya amince da zabar da Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takarar APC
  • Dan majalisar ya yi kira ga magoya bayansa da su amince da matsayar jam'iyyar sannan su daura damarar tunkarar zaben 2027

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Babban mai tsawatarwa a majalisar wakilai, Hon. Usman Bello Kumo, ya bayyana cewa ya amince da shawarar APC ta zaɓar Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha na gwamnan Gombe a zaɓen 2027.

Usman Bello Kumo, wanda shi ma yake fatan samun tikitin APC don tsayawa takarar gwamnan Gombe a 2027, ya ce matsayar tasa na tabbatar da fifikon jam’iyya ne sama da kowa.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso da Obi, NDC ta fadi 'yan takarar da za ta tsaida a 2027

Usman Bello Kumo ya amince da Jamilu Isiyaku Gwamna
Usman Bello Kumo tare da Jamilu Isiyaku Gwamna Hoto: Malam Usman Bello Kumo
Source: Facebook

Usman Bello Kumo ya amince da zabin APC

Usman Bello Kumo wanda ke wakiltar mazabar Akko ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.

Ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da dokar zaɓe ta 2025 (wadda aka yi wa gyaran fuska), wacce ta ba da damar yin amfani da tsarin maslaha a zaɓen fitar da gwani; don haka, yana goyon bayan ɗaukar wannan tsarin a jihar Gombe.

Bello Kumo ya goyi bayan APC

“Gabanin babban zaɓen 2027, babbar jam’iyyarmu, APC, tana ta shirye-shirye da nufin tabbatar da nasarar zaɓe da kuma samun nasarar jam’iyyar a zaɓuka masu zuwa."
“Sha’awata da burina na tsayawa takarar gwamna a jihar Gombe ba ɓoye suke ba. Na jira matsayar jam’iyyar cikin ɗaukar ɗamara, ko za ta ɗauki tsarin zaɓen kato bayan kato ne ko na maslaha don tikitin takarar gwamna na APC, domin ba ni damar shiga takarar gwamna mai zuwa."

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

“Sai dai, kasancewar an ɗauki tsarin maslaha kuma aka tabbatar da shi bisa ƙa’ida daidai da matsayar jam’iyyar, ba ni da wani zaɓi da ya wuce na bi umarnin jam’iyya."
“A matsayina na ɗan jam’iyya mai biyayya, ina so na nuna cikakken goyon baya da amincewa ga tsari da sakamakon babban taron APC na jihar Gombe da aka kammala, wanda ya samar da ɗan takarar maslaha kuma jagora a tseren takarar gwamna a jihar Gombe."
“Ina kira ga ɗimbin magoya bayana da masu biyayya gare ni a faɗin jihar da su bi matsayar jam’iyyar, sannan su ɗaura ɗamara don yin aiki don tabbatar da nasarar dukkan ’yan takararmu a zaɓubbuka masu zuwa."

- Usman Bello Kumo

Usman Bello Kumo ya amince da zabin APC a Gombe
Usman Bello Kumo tare da Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe Hoto: Malam Usman Bello Kumo
Source: Facebook

Jamilu Gwamna ya nemi hadin kai

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Dr. Jamil Isiyaku Gwamna, ya yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar.

Dr Jamil Isiyaka Gwamna, ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su manta da sabanin da ke tsakaninsu, su hada kai don tunkarar zaben 2027.

Jamilu Gwamna ya bukaci tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami da sauran wadanda suka nuna sha'awar takara su jingine duk wani sabani don ciyar da APC gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng