An Yi Rashin Babban Malamin Musulunci a Maiduguri, Sheikh Dazigau Tijjani
- Wani fitaccen malamin addinin Musulunci ya rasu a Maiduguri ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026 da muke ciki
- Wani matashi, Ibn Maigana ya sanar da rasuwar malamin, yana bayyana shi a matsayin mashahurin malami da ya ilmantar tare da tasiri ga al'ummar Bolori
- Bayan rasuwarsa, jama'a sun ci gaba da yi masa addu'a, yayin da aka tuna gudummawarsa ga addini, ilimi da tarbiyyar al'umma a Maiduguri da kewaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mallam Haruna Dazigau Tijjani, ya riga mu gidan gaskiya lamarin da ya tayar da hankali a yankin.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an riga an yi jana'izarsa ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026, a unguwar Bolori da ke Maiduguri.

Source: Original
Wani daga cikin ƴaƴan abokin marigayin, Ibn Maigana, ne ya sanar da rasuwar malamin ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana shi a matsayin malami mai girma.
Wani malami ya rasu a Lagos
Duniyar Musulunci ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar malamin addini a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya lamarin da ya jawo jimami a tsakanin al'ummar yankin.
Sheikh Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila ya rasu ranar Asabar a asibitin LASUTH, lamarin da ya girgiza al'ummar Musulmi.
Ɗansa Ibikunle Lateef ne ya sanar da rasuwarsa ta shafin Facebook, sannan aka yi jana'izarsa a Iponri Central Mosque bisa koyarwar addinin Musulunci.

Source: Facebook
Gudunmawar da marigayi Dazigau ya bayar
Ibn Maigana ya ce marigayin ya koyar da mutane da dama, kuma darussansa sun yi tasiri sosai ga al'ummar Bolori da sauran mazauna Maiduguri.
An gudanar da jana'izarsa da misalin karfe hudu na yamma a gidansa da ke titin Goni Tijjani a Bolori, bisa koyarwar addinin Musulunci.
Ibn Maigana ya bayyana cewa marigayin yana da kyakkyawar alaka ta dangi da mahaifinsa, lamarin da ya sa rasuwar ta kasance abin jimami gare shi.
A cikin sakonsa ya rubuta cewa:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan sanarwa ce ta rasuwar Malam Haruna Tijjani Dazigau, fitaccen malamin addini a Bolori wanda ya koyar da yawancinmu ta hanyoyi daban-daban.
"An tsara jana'izarsa da karfe 4:00 na yamma a gidansa da ke Bolori, Maiduguri, a kan titin Goni Tijjani.
"Kafin rasuwarsa, Malam ya kasance dan uwa kuma aminin mahaifina. Allah Ya jikansa da rahama."
Maigana ya bukaci al'umma su ci gaba da yi wa marigayin addu'ar samun rahamar Allah, yana mai cewa tasirin da ya bari ya zarce iyakar karatun addini.
Babban limami ya bar duniya a Kwara
Mun ba ku labarin cewa An shiga jimami bayan rashin babban limami a addinin Musulunci wanda ya bayar da gudummawa sosai.
An ce limamin Shonga, Alhaji Jibril Baba Nnatakun, ya rasu a Kwara, lamarin da ya jawo alhini daga al'ummar Musulmi.
Jagoran siyasar Kwara ta Arewa, Mohammed Baba Ibrahim, ya bayyana marigayin a matsayin malami mai hikima da sadaukarwa ga addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng

