Jam'iyyar APC Ta Fasa Tantance Shugaba Tinubu don Shiga Zaben Fitar da Gwani

Jam'iyyar APC Ta Fasa Tantance Shugaba Tinubu don Shiga Zaben Fitar da Gwani

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu rangwame daga wajen jam'iyyar APC a shirinsa na sake samu mulkin Najeriya
  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa babu bukatar tantance shugaban kasar domin shiga zaben fitar da gwani da za ta gudanar
  • Sakataren yada labarai na APC na kasa, Felix Morka, ya bayyana cewa kwamitin NWC ne na jam'iyyar ya cimma wannan matsayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yafe wa Shugaba Bola Tinubu dukkan buƙatun tantancewa domin shiga zaben fitar da gwani da za ta gudanar.

APC ta ɗauki Shugaba Tinubu a matsayin wanda aka riga aka tantance daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar domin shiga zaɓen fitar da gwani mai zuwa.

APC ta yi wa Tinubu afuwa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sakataren yaɗa labarai naAPC na kasa, Felix Morka, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso da Obi, NDC ta fadi 'yan takarar da za ta tsaida a 2027

APC ba za ta tantance Tinubu ba

Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na APC ya ɗauki wannan shawarar ne a zamansa na 188 da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.

Ya ce an ɗauki matakin ne bisa ikon da aka ba NWC a ƙarƙashin sashi na 13.4 (xiii) da (xiv) na kundin tsarin mulkin APC na tsarawa da sanya ido kan zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar, sannan a cikin wasu yanayi na musamman, ta bayar da rangwame don maslahar jam’iyyar.

Meyasa APC ta yi wa Tinubu sassauci?

“Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar APC a zamansa na 188 da aka gudanar a yau 6 ga watan Mayu, 2026, ya yanke shawarar yafe wa, sannan ya yafe wa Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, buƙatun tantancewa, kuma ya ɗauke shi a matsayin wanda aka tantance daidai da tsarin mulkin jam’iyyar domin shiga zaɓen fitar da gwani mai zuwa."

Kara karanta wannan

An yaye daga ADC, 'yan majalisa 17 sun bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC

“An ɗauki wannan shawarar ne bisa ikon da aka ba NWC a ƙarƙashin sashi na 13.4 (xiii) da (xiv) na kundin tsarin mulkin APC na tsarawa da sanya ido kan zaɓubbukan fitar da gwani na jam’iyyar, sannan a cikin wasu yanayi na musamman, ta bayar da rangwame don maslahar jam’iyyar."
“NWC ta lura cewa shugaban ya samu amincewa mai girma da ƙuri’ar kwarin gwiwa daga muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, waɗanda suka haɗa da ƙungiyar gwamnonin APC (PGF), shugabanni da mambobin majalisar dokoki ta ƙasa, da sauran rassan jam’iyyar a taron ƙoli na APC na ranar 22 ga Mayu, 2025, da ma sauran muhimman tarukan jam’iyyar."
“Haka kuma an lura cewa, a matsayinsa na shugaban ƙasa mai ci, kuma jagoran jam’iyyarmu mai girma, wanda aka riga aka tantance tare da amincewa da shi gabanin zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na 2022, buƙatar ya bayyana a gaban kwamitin tantancewa a wannan lokacin abu ne da ba shi da amfani kuma ba buƙatarsa ake yi ba."

- Felix Morka

APC ta yafewa Tinubu tantancewa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Umahi ya saka hannu a fom din Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, rattaba hannu kan fom din neman tsayawa takara na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

David Umahi Ya bayyana cewa fam ɗin neman takarar na wa'adi biyu wata muhimmiyar alama ce a tafiyar ci gaban Najeriya.

Umahi ya jaddada cewa jagorancin Tinubu ya haifar da manyan sauye-sauye a ɓangaren ababen more rayuwa, musamman a gina da gyaran hanyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng