Bayan Mika Fom din Tinubu, APC Ta Fadi Tsarin Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa
- Jam'iyyar APC na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaben 2027 yayin da masu neman takara ke dawo da fom din da suka cika
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya mayar da fom dinsa na neman takara a zaben 2027 domin yin wa'adi a kan madafun iko
- Jam'iyyar APC ta sanar da tsarin da za ta bi domin gudanar da zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta bayyana shirinta kan zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC babban zaɓen 2027 zai fito ne ta hanyar tsarin zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026, yayin miƙa fom ɗin na gani ina so da na tsayawa takara na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shettima ya mika fom din Tinubu
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya miƙa fom ɗin a madadin Shugaba Tinubu, wanda ya je ziyarar aiki zuwa ƙasashe uku.
Bisa tanadin dokar zaɓe ta 2026, ’yan takara na muƙaman zaɓe za su iya fitowa ne ta hanyar zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ko kuma ta hanyar tsarin maslaha.
Bincike ya nuna cewa Shugaba Tinubu, wanda tuni masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka amince da shi, zai nemi ƙuri’u masu zabe, tare da wani jigo na jam’iyyar APC daga jihar Delta, Stanley Osifo, wanda shi ma ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa.
Sanata Basiru ya ce jam’iyya mai mulki ta ƙuduri aniyar cika maganarta kan haɓaka dimokuraɗiyyar cikin gida, inda ya lura cewa “APC ce kaɗai jam’iyyar siyasar da ta ke tafiya da kowa da kowa.", shafin @NigAffairs ya sanya bidiyon jawabin a X.
Shugaba Tinubu ya samu yabo
Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima ya shaida wa taron gwamnoni, ministoci, da mambobin kwamitin gudanar na kasa (NWC) cewa nasarorin da Tinubu ya samu a cikin shekaru uku da suka gabata sun tabbatar da cewa yana da ƙwarewar kawo sauyi mai kyau a rayuwar ’yan Najeriya.

Source: Twitter
Tun da farko a cikin jawabinsa, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana irin ta Shettima, inda ya lura cewa Najeriya tana fama da rikicin tattalin arziki kafin Tinubu ya hau mulki.
Shugaban na APC na ƙasa ya ce sake ba Tinubu tikiti zai zama lada ne ga iyawarsa ta nuna aminci ga alkawuran da ya ɗauka, kamar yadda yake a cikin shirinsa na "Renewed Hope Agenda".
APC ta fasa tantance Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi wa Shugaba Bola Tinubu, babban gata kan zaben 2027.
Jam’iyyar APC ta yafe wa Shugaba Bola Tinubu dukkan buƙatun tantancewa domin shiga zaben fitar da gwani da za ta gudanar.
APC ta ɗauki Shugaba Tinubu a matsayin wanda aka riga aka tantance daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar domin shiga zaɓen fitar da gwani mai zuwa.
Asali: Legit.ng

