Hankula Sun Tashi da Bam Ya Fashe a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

Hankula Sun Tashi da Bam Ya Fashe a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

  • An samu fashewar wani bam da aka da sa a kan hanyar da ababen hawa ke wucewa a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara
  • Mazauna yankin sun yi zargin cewa 'yan bindiga ne suka dasa bam din wanda fashewarsa ta jawo sanadiyyar rasa rayuka tare da jikkata wasu mutane daban
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta bayyana namijin kokarin da ta yi wajen dawo da doka da oda a yankin tare da tabbatar da cewa ta dauki matakan da suka dace

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - An tabbatar da mutuwar mutane shida sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a jihar Zamfara.

Wasu mutane shida sun samu raunuka sakamakon fashewar bam din da binne a kan hanyar Bagega zuwa Anka da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin Arewa da suka fitar da wadanda za su gaje su a zaben 2027

Bam ya kashe mutane a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.

Bam ya kashe mutane a Zamfara

Lamarin ya auku ne lokacin da wata motar kasuwanci mai ɗauke da fasinjoji ta bi ta kan bam din, lamarin da ya haddasa babban rashi.

A cewar majiyoyin yankin, ana zargin wasu ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin ne suka binne bam din a kan hanyar.

Wani mazaunin garin Bagega, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce fashewar ta faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe ranar Alhamis, inda ya ƙara da cewa wasu daga cikin fasinjojin da ke cikin motar sun mutu, yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka.

Me 'yan sanda suka ce?

Tashar Channels tv ta ce kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya shaida mata cewa sauran mutane shidan suna karɓar magani sakamakon raunuka daban-daban da suka ji.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a garuruwan jihar Kogi, an rasa rayukan mutane masu yawa

Yazid Abubakar ya bayyana cewa rundunar ta tura tawagar kwararru kan abubuwan fashewa (EOD) zuwa wurin da abin ya faru nan take, domin tabbatar da tsaron yankin da kuma hana sake samun wasu asarar rayukan.

'Yan bindiga sun dasa bam a Zamfara
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

A cewarsa, jami’an EOD sun gudanar da cikakken bincike a kan hanyar don gano tare da lalata duk wani ƙarin bam da aka binne kafin a sake buɗe hanyar don amfanin jama’a.

“A halin yanzu an dawo da doka da oda. An tura tawagar jami’anmu na EOD zuwa yankin don bincika duk faɗin wurin domin tabbatar da cewa ba a sake binne wani abin fashewar ba."

- Yazid Abubakar

'Yan bindiga sun kona fadar basarake a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin tamuwar gayya bayan jami'an tsaro sun samu nasara a kansu.

Tsagarun 'yan bindigan sun kai harin ramuwar gayyar ne a ƙauyen Yankuzo da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kona fadar Hakimin yankin, Alhaji Babangida Hamza, tare da sace kayayyaki masu daraja yayin farmakin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng