Bayan Pantami, Goje da Sanata Alkali Sun Yi Watsi da 'Yan Takarar APC a Gombe
- Jam'iyyar APC mai mulki a Gombe ta fara fuskantar sabani bayan gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya zabi dan takarar da yake so ya gaje shi
- Sanata Muhammadu Danjuma Goje da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a majalisar dattawa ya yi watsi da fitar da 'yan takara da gwamnan ya yi
- A daya bangaren, tsohon ministan sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali da a yanzu haka ya ke neman taarar gwamna ya nesanta kansa da lamarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya yi watsi da tsarin hadin kai da jam’iyyar APC ta Jihar Gombe ta dauka na fitar da 'yan takara.
Rahotanni sun nuna cewa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya fitar da 'yan takara a matakan gwamna, majalisun tarayya da jihohi da sauransu.

Source: Facebook
Martanin Sanata Danjuma Goje
Daily Trust ta ruwaito cewa jiga-jigan jam’iyyar, karkashin jagorancin Inuwa Yahaya sun amince da DCP Mohammed Ahmadu Deba (mai ritaya) a matsayin ɗan takarar APC domin maye Sanata Goje a 2027.
Sai dai a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Saidu Mu’azu Kumo ya fitar, Sanata Goje, wanda ke neman wa’adi na biyar a Majalisar Dattawa, ya ce taron hadin kan da aka yi bai zama cikakke ba.
Ya ce:
“Bai hada da dukkan ‘yan takarar da aka amince da su a cikin jam’iyyar ba.”
A cewarsa, dokar zaɓe ta tanadi hanyoyi biyu na doka da jam’iyyun siyasa za su bi wajen fitar da ‘yan takara domin gabatar wa Hukumar INEC gabanin zaɓen 2027 kuma ba a bi su ba.
Martanin Sanata Alkali a Gombe
Sanata Saidu Ahmed Alkali ya yi watsi da batun ɗan takarar hadin kai da gwamna da wasu 'yan a APC a Jihar Gombe suka amince da shi.

Kara karanta wannan
Sanata ya daina jayayya, ya bi bayan dan takarar gwamna da Zulum ya tsayar a Borno
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Fecebook, Saidu Alkali ya ce wannan mataki ya saba da dimokuradiyya, son rai ne, kuma ya ci karo da dokar zaɓe ta 2026.

Source: Facebook
Ya ce sayen takardun nuna sha’awa da na takara da ya yi ya tabbatar da shi a matsayin ɗan takara da ya kamata a ba shi damar shiga tattaunawa kan irin wadannan muhimman batutuwa.
Saboda haka, Sanata Said Alkali ya bayyana cewa ya nesanta kansa daga wannan lamari wanda ya ce ba shi da tushe a kundin tsarin mulki ko dokoki.
Pantami ya yi watsi da matakin APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ya nuna cewa bai amince da matakin da aka dauka a Gombe wajen fitar da dan takara ba.
Sheikh Pantami ya bayyana cewa ba a bi tsarin da dokar kasa ta tsara wajen fitar da wanda zai wakilci jam'iyyar ta tsarin sulhu ba sam.
Hakan na zuwa ne bayan gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ayyana Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin wanda ya ke fatan ya gaje shi a 2027.
Asali: Legit.ng
