Malami Ya Bankado ‘Sirrin’ Tinubu Game da Neman Cin Zabe Ta Kowace Hanya

Malami Ya Bankado ‘Sirrin’ Tinubu Game da Neman Cin Zabe Ta Kowace Hanya

  • Babban fasto a Najeriya, John Onaiyekan ya bayyana damuwa kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da zaben shekarar 2027
  • Faston ya ce wasu na kusa da shugaban ƙasa na ba shi bayanai na kasa game da Najeriya, wanda bai yi daidai da halin jama'a ba
  • Ya gargadi cewa idan ba a tabbatar da zaɓe mai 'yanci da adalci ba, tare da mutunta ƙuri'un jama'a, Najeriya na iya fuskantar ƙarin matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fasto, John Onaiyekan, tsohon Akbishop na Abuja, ya bayyana damuwa game da zaben 2027 kan shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Faston ya ce gwamnatin ta kuduri aniyar ci gaba da mulki a zaɓen 2027 ta kowace hanya, ya ce albarkatun da gwamnati ke da su na iya shafar sahihanci da amincin zaɓen.

Kara karanta wannan

Ribadu: "Dabarar gwamnati na yaki da ta'addanci ya fara murkushe yan bindiga"

Fasto ya gano shirin Tinubu game da zaben 2027
Fasto John Onaiyekan da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise, kwanaki kaɗan bayan shugabannin Ƙungiyar Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN) sun gana da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Musabbabin ziyarar ƙungiyar ga Tinubu

Onaiyekan ya kuma ce wasu da ke kusa da shugaban ƙasa na gabatar masa da halin da ƙasa ke ciki, alhali hakan bai dace da irin ƙalubalen da yawancin 'yan Najeriya ke fuskanta ba.

Tawagar CBCN ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Matthew Ndagoso, ta kai ziyarar ne domin gabatar da matsayarta kan halin da ƙasar ke ciki, inda ta bayyana damuwarta game da matsalolin tattalin arziki da rayuwar al'umma.

A martaninsa, Shugaba Tinubu ya kare ayyukan gwamnatinsa, yana cewa tattalin arzikin ƙasa na samun daidaito, yajin aikin ASUU ya zama tarihi, sannan ya jaddada cewa INEC hukuma ce mai zaman kanta.

Fasto ya fadi shirin Tinubu kan zaben 2027
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da fastocin suka fadawa Tinubu

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya ba da mamaki, ya fadi gaskiya a idon Tinubu kan ta'addanci

Onaiyekan ya ce limaman sun gaya wa shugaban ƙasa cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma matsin tattalin arziki na ci gaba da jefa talakawa cikin ƙunci. Ya ce shugaban da wasu jami'ansa ba su nuna farin ciki da wannan saƙo ba.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa bai amince da bayanin limaman ba, yana mai cewa ƙasar ba ta cikin halin da suka bayyana, kuma tattalin arziki na tafiya yadda ya kamata.

Cardinal ɗin ya kuma bayyana damuwa game da zaɓen 2027, yana cewa limaman Katolika na fargabar gwamnati na son amfani da duk wata dama domin ci gaba da mulki.

Ya gargadi cewa idan ba a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci ba, tare da mutunta ƙuri'un jama'a, hakan na iya jefa ƙasar cikin sabbin matsaloli.

Tinubu zai cire tallafin lantarki

An ji cewa Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana shirin cire tallafin bangaren wutar lantarki a hankali inda za a fara daga shekarar 2027.

Game da karin kudin wuta, ministan ya ce ba za a sami karin kudin wuta ba nan take ga masu amfani da wutar lantarki a yau da kullum.

Ya ce za a cire tallafin ne daki-daki domin tabbatar da cewa ba a hana al'umma amfanin da suke samu ba, tare da daidaita bashin da ake bi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.