Zance Ya Kare: APC Ta ba Yusuf Buhari Tikitin Takara a Jihar Katsina

Zance Ya Kare: APC Ta ba Yusuf Buhari Tikitin Takara a Jihar Katsina

  • An bayyana dan tsohon dan shugaban kasa, Yusuf Buhari a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen Majalisar Wakilai na 2027 a Jihar Katsina
  • Ɗan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana neman tikitin jam’iyyar APC domin wakiltar wata mazaba a matakin tarayya a zaben 2027
  • Rahotanni sun nuna cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Yusuf Buhari a matsayin ɗan takara da zai wakilici Sandamu/Daura/Mai’adua

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari, ya fito a matsayin ɗan takarar APC da zai wakilici mazabar tarayya ta Sandamu/Daura/Mai’adua a 2027.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Yusuf ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Majalisar Wakilai a Jihar Katsina karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƴan sanda ya ƙi yarda da sulhu, ya sayi fom ɗin takarar gwamna

Yusuf Muhammadu Buhari
Yusuf Buhari na magana a gidan gwamnatin Katsina. Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

An ba Yusuf Buhari takarar majalisa a APC

Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya sanar da cewa Yusuf Buhari ya samu takara a jam'iyyar APC a sakon da ya wallafa a X.

Bashir ya sanar da cewa:

"Hon. Yusuf Muhammadu Buhari ya kasance dan takarar da aka fitar ya wakilci mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua."

Idan ba a manta ba, jiga-jigan APC a Jihar Katsina sun ƙarfafa goyon bayansu ga ɗan Muhammadu Buhari domin ƙara wa jam’iyyar damar cin zaɓe.

An ruwaito cewa gwamna Dikko Umar Radda ya ayyana Yusuf a matsayin wanda yake mara wa baya a takarar da ke tafe duk da wakilin mazabar na yanzu, Hon. Aminu Jamo dan jam’iyyar APC mai mulki ne.

Mazabar tarayya da Yusuf Buhari ke son wakilta ta ƙunshi kananan hukumomi uku: Sandamu, Daura, da Mai’adua a Jihar Katsina.

Sheikh Pantami da Yusuf Muhammadu Buhari
Sheikh Isa Ali Pantami da Yusuf Buhari a Borno. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

An bayyana cewa yankin mai matukar muhimmanci ne a siyasar Jihar Katsina, yana da unguwanni daban-daban, ciki har da Karkarku, Kwasarawa, Daneji, Fago, da Rade a karamar hukumar Sandamu.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

Ya 'yan Najeriya suka kalli takarar Yusuf?

Legit ta rahoto cewa 'yan Najeriya sun mayar da martani a kafar X yayin da aka sanar da cewa Yusuf Muhammadu Buhari ya samu tikitin APC:

@Opaconnecty ya ce:

"Hakan yana da kyau, domin girmama mahaifinsa da ya rasu. A matsayinka na uba, wane abu mai kyau kake tanada wa iyalinka?"

Shi kuma @aoidowu1309 ya ce:

"Kai! Hajiya Aisha Buhari za ta yi matukar alfahari da Yusuf. Ina fatan ba zai kunyata su ba. Da zan ba shi shawara ya yarda, da na ce masa ya bari wasu su tsaya takara."

@Tosquo kuwa cewa ya yi:

Haka ya kamata. Na taya ka murna."

Kashim Shettima ya gargadi 'yan APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi gargadi yayin da ake shirin zaben 2027.

Shettima ya bayyana cewa duk yadda za a yi mutum daya ne zai samu tikitin takara idan aka yi zaben fitar da gwani a jam'iyyar APC.

Saboda haka ya bukaci hadin kai, musamman daga dukkan wadanda ba su samu tikiti ba yana cewa dama tsarin dimokuradiyya ya gaji haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng