An Fara Bugawa: Atiku, Manyan ADC 2 Sun Saye Fom din Takarar Shugaban Kasa

An Fara Bugawa: Atiku, Manyan ADC 2 Sun Saye Fom din Takarar Shugaban Kasa

  • 'Yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban na cigaba da sayen fom domin nuna sha'awar shiga takara a babban zaben 2027 da ake magana a kan shi
  • A jam'iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar da wasu manyan 'yan siyasa sun saye fom din takarar shugaban kasa domin a fafata da su a 2027
  • Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen 2027, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa a Agustan 2026 za a fara kamfen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - 'Yan siyasa daga jam'iyyar adawa ta ADC na cigaba da sayen fom din takara yayin da ake shirye-shirye game da zaben 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rikicin jam'iyyar ADC a kotu da kuma maganganu kan wanda zai yi mata takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Bayan mika fom din Tinubu, APC ta fadi tsarin tsaida dan takarar shugaban kasa

Da Atiku Abubakar da Mohammed Hayatu-Deen
Atiku Abubakar da Mohammed Hayatu-Deen suka saye fom din ADC. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

Atiku da wadanda suka saye fom

Punch ta wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi sun saye fom din neman tsayawa takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027.

Wani mai neman takarar shugaban ƙasa, Mohammed Hayatu-Deen shi ma ya saye fom ɗin, inda ya yi alƙawarin bai wa tsaro, samar da ayyukan yi da kuma tsadar rayuwa da ke addabar miliyoyin ’yan Najeriya muhimmanci.

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya tabbatar da cewa ’yan takarar uku sun riga sun saye fom ɗin.

“Eh, su ukun nan (Atiku, Amaechi da Hayatu-Deen) sun saye fom ɗin,”

In ji shi.

Vanguard ta wallafa cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta bayyana cewa kudin fom ɗin neman tsayawa takarar shugaban ƙasa yana kan Naira miliyan 90.

Hayatu-Deen ya karɓi fom ɗin daga hannun Sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam’iyyar, Chinedu Idigo a ranar Juma’a, ya ce dole zaɓen 2027 ya mayar da hankali kan inganta tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan adawa sun dimauce da INEC ta kawo amfani da sojoji a zaɓen 2027

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Lokacin da Atiku Abubakar ya gana da Rotimi Amaechi. Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi
Source: Facebook

Jam’iyyar ADC ta sanya ranar 6 ga Mayu zuwa 13 ga Mayun 2026 domin sayar da fom ɗin neman tsayawa takarar shugaban kasa.

Maganar fara kamfen a 2027

INEC ta ce za a gudanar da zaɓen fidda gwanin jam’iyyu da warware rikice-rikicen da suka shafe su tsakanin 23 ga Afirilu da 30 ga Mayu, 2026.

A cewar hukumar, yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin ƙasa zai fara daga ranar 19 ga Agusta, 2026, yayin da na gwamnoni da majalisun dokokin jihohi zai fara daga ranar 9 ga Satumba, 2026.

An gargadi malamai kan 2027

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya yi kira ga malamai game da zaben 2027.

Farfesa Oloyede ya bukaci malaman addinin Musulunci da su guji yi wa 'yan siyasa kamfen a kam bimbari domin hakan zai jawo rabuwar kai.

Ya yi kiran ne yayin wani taron shekara-shekara da aka yi a masallacin Juma'a na Lekki da ke jihar Legas, inda aka tara malamai da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng