Da sake: Amnesty Ta Nemi a Bi Jinin Matasan Kano da aka Kashe bayan Naɗa Garo

Da sake: Amnesty Ta Nemi a Bi Jinin Matasan Kano da aka Kashe bayan Naɗa Garo

  • Kungiyar kare hakkin dan ada a duniya ta Amnesty International Nigeria bayyan kaduwa game da kisan matasa biyar da 'yan daba suka yi
  • 'Yan daban siyasa da suka halarci nadin mataimakin gwamnan Kano, Hon Nasiru Yusuf Gawuna ne suka yi aika-aikar 'barnatar da rayukan matasan
  • Kungiyar ta bayyana halin da Kanawa suka shiga saboda kokarin dawowar fadan daban siyasa yayin da ake gab da fara harkokin neman zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya Amnesty Int'l ta buƙaci hukumomin Najeriya su gaggauta gudanar da bincike kan kashe mutane biyar da aka yi a jihar Kano.

Kungiyar ta yi takaicin kisan matasan wanda ta danganta da 'yan daban siyasa a ranar Talata 5 ga watan Mayu na shekarar 2026, inda suka yi danyen aikin bayan rantsar da mataimakin gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya bi sahun Kwankwaso, ya bayyana dalilinsa na barin ADC

Amnesty ta nemi a binciki kisan matasan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Murtala Sule Garo, Abdullahi Ganduje da manyan Kano a wajen rantsar da Garo Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

A wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba 6 ga watan Mayu, 2026, ta bayyana cewa harin ya nuna yadda tashin hankalin siyasa ke ƙara muni a jihar Kano.

Amnesty na fargabar dawowar fadan daban siyasa

Amnesty Int'l ta bayyana lamarin a matsayin mafi muni daga hare-haren daba na siyasa da aka gani cikin shekarun baya-bayan nan.

Ƙungiyar ta ce bidiyon da ta bincika sun nuna wasu mutane masu ɗauke da makamai suna tafiya cikin rukuni-rukuni, suna bin mutanen da ke ƙoƙarin tserewa kafin su kashe su a kan tituna.

Amnesty ta ce kisan matasan ya dawowar tsoron fadan daban siyasa
Taswirar jihar Kano da ake fargaba za a dawo da fadan siyasar daba Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sauran bidiyoyin kuma, a cewar Amnesty Int'l sun nuna gawarwakin waɗanda aka kashe kwance cikin jini bayan harin da ya daga hankulan jama'a.

Ƙungiyar ta kuma ce an ga waɗanda ake zargi da kai harin sanye da kayan da ke da alaƙa da jam’iyya mai mulki tare da yin kalaman barazana da tayar da hankali.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso da Obi, NDC ta fadi 'yan takarar da za ta tsaida a 2027

Ta ƙara da cewa akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu magoya bayan siyasa na kai hare-hare kan abokan hamayya, ko waɗanda ake zargin suna adawa da su.

Muna binciken kisan matasan Kano - Amnesty Int'l

Amnesty ta bayyana cewa tana binciken zarge-zargen da ke cewa wasu fitattun ƴan siyasa da jami’an gwamnati a Kano na iya kasancewa da hannu a rikicin.

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce:

“Dole ne hukumomin Najeriya, ƴan siyasa da jam’iyyun siyasa su mutunta doka tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi kafin, lokacin da kuma bayan tarukan siyasa.”

Ta kuma bayyana damuwa cewa lamarin na tauye haƙƙin jama’a, tana mai cewa:

“Ya kamata a tabbatar da kare haƙƙin jama’a na zirga-zirga cikin ’yanci.”

A cewarta:

“Ƙaruwar hare-haren siyasa da ƴan daba masu makamai ke yi domin wasu ƴan siyasa a Kano na haifar da yanayi na tsoro tare da tauye haƙƙin jama’a na shiga siyasa cikin ’yanci.”

An kashe matasa a Kano

A baya kun samu labarin cewa hankulan iyaye da wasu bayin Allah sun tashi a jihar Kano awanni kadan bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

An yaye daga ADC, 'yan majalisa 17 sun bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe matashi Nura Ribadu a harin da ake zargin ’yan daban siyasa sun kai masa har cikin wani asibiti daga bisani aka kashe wasu karin matasa hudu duka yan Dandago.

Kisan Nuhu ya faru ne a harabar Kano Medical Centre bayan rantsar da sabon mataimakin gwamna inda aka ga matasa rike da mugayen makamai sun zage matashin suna bugunsa ta kowane bangare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng