'Farfaganda Ce": Atiku Ya Zargi Gwamnati da Jefa Najeriya a Wahala

'Farfaganda Ce": Atiku Ya Zargi Gwamnati da Jefa Najeriya a Wahala

  • Atiku Abubakar ya ce babu wata farfaganda da za ta iya ɓoye tsananin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta
  • Ya kalubalanci gwamnatin Bola Tinubu kan ci gaba da karɓo bashi duk da ikirarin ƙaruwa a kudaden shiga da cire tallafin mai
  • 'Dan takarar shugaban ƙasar ya shaida wa gwamnati abin da ya kamata a mayar da hankali a kai ba batun kokarin kare sunanta a idon jama'a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi watsi da kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da fadar shugaban ƙasa ke yi.

Ya bayyana cewa dukkanin maganganin da ke fito wa daga bakin gwamnati farfaganda ce da ba za ta iya ɓoye irin wahalar da miliyoyin 'yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

Atiku Abubkar ya zargi gwamnati da farfaanda
Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar kalamai tsakanin Atiku da fadar shugaban ƙasa kan sauye-sauyen tattalin arziki, cire tallafin man fetur, karɓo bashi da kuma manufofin haraji.

Kalaman gwamnatin Tinubu kan Atiku

Daily Post ta kawo labarin cewa Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce daya daga cikin manyan ribar cire tallafin mai ita ce ƙaruwar kudin shiga da aka raba wa rukunan gwamnati.

Sai dai a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, 2026 Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da dogaro da dadin baki wajen magance matsalar.

Atiku ya ce tambayar da gwamnatin ta kasa ba da amsa ita ce,:

"Idan tattalin arzikin ƙasa yana tafiya da kyau, me ya sa 'yan Najeriya ke ƙara talaucewa?"

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

Ana fama da talauci - Atiku

Ya ce yayin da gwamnati ke yabon ci gaban wasu alkaluman tattalin arziki, talakawa na fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashi da kuma raguwar ƙarfin saye.

Atiku Abubakar ya ce har yanzujama'a na cikin bakin talauci
Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar ADC a zaben 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Ya ce:

"Gwamnati tana murnar alkaluman tattalin arziki sun karu, amma talakawa na fama da matsalolin rayuwa. Tana magana da alfahari kan ci gaban GDP yayin da iyalai ba sa samun abinci. Tana yabon sauye-sauye alhali miliyoyin mutane na ƙara fadawa cikin talauci."

Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati da yadda rayuwar jama'a ta inganta, ba wai da alkaluman tattalin arziki kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng