'Atiku da Amaechi, Peter Obi da Kwankwaso ba Za Su Iya Samun Nasara a Zaben 2027 ba'
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce tikitin Atiku/Amaechi da Obi/Kwankwaso ba za su iya kayar da Tinubu da Shettima a zaɓen 2027 ba
- Ya soki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi kan burinsu na siyasa
- Wike ya kare sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, musamman kawo karshen tallafin man fetur wanda ake ganin ya kawo wahalar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana kwarin gwiwa kan nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Wike ya ce tikitin takarar shugaban kasa na Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi, da kuma na Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, ba za su iya kayar da tikitin Tinubu da Shettima ba.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa ta wata-wata da manema labarai, inda ya ce ‘yan takarar adawa ba su da karfin da za su iya fuskantar Tinubu.
Wike ya dura kan Atiku da Amaechi
Ministan ya yi watsi da burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ke neman takara karkashin ADC, tare da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin abokin takara.
Ya ce wannan hadin gwiwar ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa ba shi da karfin da zai kai su ga nasara.
Wike ya kuma yi magana kan dan takarar NDC, Peter Obi, inda ya bayyana cewa shirye-shiryensa na siyasa ba za su yi nasara ba, cewar rahoton Vanguard.
Ya kare manufofin gwamnatin Tinubu
Yayin da yake kare sauye-sauyen gwamnatin Shugaba Tinubu, Wike ya ce manufofin gwamnati da shirye-shiryen gyara tattalin arziki sun zama wajibi domin magance matsalolin da aka kwashe shekaru ana fama da su.
Tsohon gwamnan Ribas ya ce Tinubu ya nuna jarumtar siyasa da gwamnatocin baya suka kasa nunawa, musamman wajen kawo karshen tallafin man fetur wanda ya ce yana cin dimbin kudaden kasa.

Source: Facebook
Ya zargi Obi da yin siyasar tausayi
Wike ya ce yana son shugabanni wadanda ayyukansu suka dace da alkawuran da suke yi, inda ya soki yadda Peter Obi ke gudanar da wasu harkokinsa na siyasa.
Ya zargi Obi da yin abin da ya kira “siyasar tausayi”, yana mai cewa wasu ayyukansa na neman jawo hankalin jama’a ne maimakon nuna cikakken shugabanci.
Ya ce:
"Na san Peter Obi sosai. Ba na son mutane masu neman daukar hankalin jama’a kawai. Ban taba yin bikin ranar haihuwata a sansanonin ‘yan gudun hijira ko gidajen marayu ba saboda ina son tausayi daga jama’a.”
Wike ya taɓo tsohon gwamna, Amaechi
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana yadda siyasar tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, take a yanzu.
Wike ya bayyana shi a matsayin dan siyasar da ya rasa tasiri, yana mai cewa ba shi da wata kima ta zabe a Ribas da ma yankin Kudu maso Kudu.
Ministan ya ce tun bayan zaben 2011, Amaechi bai taba jagorantar wani dan takarar shugaban kasa zuwa nasara ba.
Asali: Legit.ng
