Dan Majalisar Tarayya Ya Rasa Tikitin APC, An ba 'Dan Fitaccen Attajiri a Jihar Katsina

Dan Majalisar Tarayya Ya Rasa Tikitin APC, An ba 'Dan Fitaccen Attajiri a Jihar Katsina

  • Hon. Sani Aliyu Danlami, mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar wakilai ya rasa tikitin neman takara karo na uku a zaben 2027
  • Jam'iyyar APC ta jihar Katsina ta bai wa dan fitaccen attajiri, Alhaji Dahiru Mangal takara a mazabar, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce
  • Abba Dahiru Mangal ya zama dan takarar APC ne bayan shafe kwanaki ana zaman sulhu tsakanin masu neman takara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Hon. Sani Aliyu Danlami, ya rasa tikitin jam’iyyar APC na sake tsayawa takara a zaben 2027.

Danlami, wanda ke wa’adinsa na biyu a majalisar wakilai, ya sha kaye ne bayan tattaunawa mai zafi da aka shafe kwanaki ana yi tsakanin manyan jiga-jigan APC da kwamitin sulhu na mazabarsa.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Abba Mangal.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda lokacin da yake mika wa Abba Mangal fam din takara a inuwar APC Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

APC ta ba 'dan Mangal takara a Katsina

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kwamitin sulhu da Gwamna Dikko Radda ya kafa, ya amince da Abba Mangal, daya daga cikin ’ya’yan fitaccen attajiri, Dahiru Mangal, a matsayin dan takarar APC.

Wannan mataki ya nuna babban sauyi a siyasar mazabar Katsina ta Tsakiya, bisa la’akari da matsayin Danlami na dan majalisa mai ci da kuma karfinsa a matakin kasa.

Haka zalika, nasarar Abba Mangal, wanda lauya ne, ta jawo ce-ce-ku-ce domin bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba kafin wannan lokaci.

Hon. Danlami ya amince da sakamakon

Hon. Danlami ya amince da sakamakon tsarin sasanci da aka bi, inda ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu bin doka da oda, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

A wata sanarwa da ya fitar, ya gargadi ’yan jam’iyya APC da su guji tashin hankali tare da fifita zaman lafiya da hadin kai domin tabbatar da daidaito a jihar Katsina da kuma jam’iyyarsu.

Kara karanta wannan

Sanata ya daina jayayya, ya bi bayan dan takarar gwamna da Zulum ya tsayar a Borno

Yadda aka gudanar da zaben

Majiyoyi sun bayyana cewa tattaunawar ta dauki kwanaki biyu, daga Talata zuwa Alhamis, inda aka gudanar da zaman sulhu tsakanin masu neman tikitin da magoya bayansu.

Daga cikin wadanda suka nemi tikitin har da Lawal Amadu Joka, tsohon hadimin tsohon gwamna Aminu Bello Masari; Haruna Maiwada; Ibrahim Ali Guguwa; Sani Danlami; da Hon. Abdurashid Abba.

Abba Mangal.
Abba Dahiru Magal a wurin taron da APC ta shirya domin raba fam da yan takararta a gidan gwamnatin jihar Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Tasirin Dahiru Mangal a Katsina

Dahiru Mangal na daya daga cikin manyan masu tasiri a siyasar jihar Katsina, inda karfinsa ya fara bayyana tun fiye da shekaru 20 da suka gabata.

An danganta shi da rawar da ya taka wajen nasarar marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua a zaben gwamnan jihar a 2003.

Tun daga lokacin, ana ganin yana taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukunci kan mukamai da zabubbuka a fadin jihar Latsina

Duk da haka, wannan ne karon farko da wani daga cikin iyalansa ya zama dan takara a zaben siyasa.

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Yusuf Buhari ya samu takara a APC

A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana Yusuf Buhari a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen Majalisar Wakilai na 2027 a Jihar Katsina.

Yusuf, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ya zama ɗan takarar APC da zai fafata a mazabar tarayya ta Sandamu/Daura/Mai’adua a zaben 2027.

Tun garko dai jiga-jigan APC a Jihar Katsina ciki har da Gwamna Dikko Radda sun nuna goyon bayansu ga ɗan Muhammadu Buhari domin ƙara wa jam’iyyar damar cin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262