Yusuf Buhari Ya Faɗi Dalilinsa na Tsunduma Harkar Siyasa, Ya Tuna Mahaifinsa

Yusuf Buhari Ya Faɗi Dalilinsa na Tsunduma Harkar Siyasa, Ya Tuna Mahaifinsa

  • Ɗan marigayi tsohon shugaban kasa, Yusuf Buhari ya bayyana yadda ya shiga siyasa duk da cewa tun farko bai yi niyyar tsunduma ba
  • Ya ce ya amsa kiraye-kirayen al’umma ne bayan ganin irin gudummawar da mahaifinsa ya bayar tun daga soja zuwa mulkin farar hula
  • Yusuf ya yi alƙawarin taimaka wa matasa da ayyukan yi, yana mai cewa rashin aikin yi shi ne babban ƙalubale, ya kuma yaba dokar bai wa matasa damar takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Ɗan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan shiga siyasa a rayuwarsa.

Yusuf Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya tsunduma a harkar siyasa wanda tun farko bai yi tsammani ba.

Yusuf Buhari ya magantu kan dalilin shiga siyasa
Dan marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari yana jawabi yayin taro. Hoto: Yusuf Buhari.
Source: Twitter

Yusuf Buhari ya magantu kan siyasarsa

Matashin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DW Hausa wanda shafin ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar sulhu, Trump ya yi barazana mai ɗaga hankali ga Iran

A cikin bidiyon, Yusuf Buhari ya tuna gudummawar da mahaifinsa ya ba Najeriya tun daga mulkin soja har zuwa farar hula.

Yusuf ya ce dole ya dawo gida domin ganin yadda rayuwar al'umma ke tafiya saboda ba da tashi gudummawa a ƙasa.

Ya ce:

"Ni kaina tun tuni nake fada, ba zan taba shiga siyasa ba, amma ga shi yanzu na shiga.
"Maganar gaskiya na amsa kiraye-kirayen al'umma ne, na ga ayyukan da mahaifina ya fara tun lokacin da ya shiga soja yana bautawa kasa.
"Na ga ya kamata na kyautata wa al'umma ni ma na ba da tawa gudunmawa shi ne na ce bari na dawo gida."
Yusuf Buhari ya tuna gudunmawar da mahaifinsa ya bayar
Yusuf Buhari da mahaifinsa marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: @MBuhari.
Source: Twitter

Alkawarin da Yusuf Buhari ya yi ga al'umma

Yusuf ya sha alwashin inganta rayuwar matasa wurin ba su ayyukan yi inda ya ce wannan shi ne babbar matsala a yanzu.

Ya ce abin alfahari ne yadda mahaifinsa ya tabbatar da doka wacce ta ba matasa daman tsayawa takara daga shekara 25 ya yi sama domin damawa da su.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Zaben shugaban kasar Najeriya zai yi zafi kamar yaki a 2027

"Da yardar Allah muna shigowa, za mu samu yadda za mu yi mu sama wa matasa aikin yi domin shi ne matsalar mu a yanzu.
"Mahaifina ya riga ya sanya hannu a dokar takara, daga shekara 25 ya yi sama mutum zai iya neman takarar dan majalisa.
"Tun da ina neman wanan kujera dole in dawo cikin jama'a, da yadda ayyukan suke tafiya, dole sai kazo kasa ido ka ga abubuwan da kake aiwatarwa ana yinsu ko ba a yi."

Yusuf Buhari

Yusuf Buhari ya gana da Gwamna Radda

Mun ba ku rahoton cewa masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Daura sun gabatar da Yusuf Muhammadu Buhari ga gwamna Dikko Radda na jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake maganar cewa ya dace Yusuf Buhari ya tsaya takarar Majalisar wakilai a zaben 2027 da ke tafe.

A yayin taron, gwamna Dikko Radda ya bukaci a cigaba da bin tsari da tuntubar jama’a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.