Sauki Ya Zo: Matatar Dangote Ta Yi Rangwame a Farashin Man Fetur da Dizal a Najeriya

Sauki Ya Zo: Matatar Dangote Ta Yi Rangwame a Farashin Man Fetur da Dizal a Najeriya

  • Matatar Dangote da ke jihar Legas ta sauke farashin kowace litar man fetur daga N1,215 zuwa N1,165 a Najeriya domin saukaka wa mutane
  • Rahotannin da suka fito yau Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026 sun ce an rage farashin dizal daga N1,650 zuwa N1,570 kan kowace lita
  • Sabon sauyin ya nuna raguwar N50 a fetur da N80 a dizal, wanda ake ganin wata alama ce da samun sauki ga yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legas, Nigeria - Matatar Dangote da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya ta yi sabon rangwwme a kan farashin man fetur (PMS) da man dizal domin rage wa jam's radadi.

Matatar hamshakin dan kasuwar kuma wanda ya fi kowa arziki a Afirka ta rage farashin da take bai wa yan kasuwa sarin fetur daga N1,215 zuwa N1,165 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Dalilan EFCC na garkame asusun gwamnatin Osun kafin zabe

Fetur.
Yadda ake hada hadar man fetur a gidan mai a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ce ta tabbatar wa Tribune Online cewa matatar ta kuma rage farashin dizal (AGO) daga N1,650 zuwa N1,570 kan kowace lita.

Dangote ya rage farashin fetur da dizal

Sabon sauyin ya nuna an rage farashin fetur da N50 a kowace lita, yayin da aka rage farashin dizal da N80 a kowace lita.

Ana sa ran ƙarin bayanai za su fito nan gaba kan sabon tsarin farashin da sauran bayanan da suka shafi wannan sauyi.

Dangote ya bayyana dalilin rage farashin

A wata sanarwa da Kamfanin Dangote Group ya fitar ranar Laraba, matatar ta ce an yi wannan sauyi ne domin rage tsadar makamashi, inganta samun kayayyakin mai da kuma tallafa wa ayyukan tattalin arziki a faɗin Najeriya.

Kamfanin ya ce matakin ya sake tabbatar da kudurinsa na samar da kayayyakin mai masu inganci da araha ga kasuwar Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya tubure kan dokar gwamnatin Tinubu na hana wa'azi, ya sha alwashi

Matatar Dangote Refinery ta bayyana cewa za ta ci gaba da tabbatar da wadataccen mai tare da amfani da ingantaccen tsarin aiki domin samar da ƙima ga masu amfani, 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki.

Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Aliko Dangote
Source: Getty Images

Ta kuma ce idan yanayin kasuwa ya ba da dama, za ta ci gaba da mika amfanin da take samu daga ingantaccen aiki ga masu amfani ta hanyar rage farashi.

Matatar ta ce za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi a Najeriya, rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa ta hanyar samar da kayayyakin mai masu inganci.

Wani mai sana'ar sayar da fetur a bakin hanya a Katsina, Kabiru Dogo ya tabbatar wa Legit Hausa cewa an rage farashin fetur a gidajen mai amma bai kai N50 ba.

Ɗan bunburutun ya ce lokacin da ya je sayen mai a ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2026, ya taras farashin ya sauka daga N1350 zuwa N1,330, watau an samu ragin N20.

"Eh na fahimci an aamu sauki amma gskiya N20 suka rage mana, a baya mun sayan kowace lita N1,350, yanzu kuma ya dawo N1,330. Muna fatan nan gaba kadan a kara samun ragi," in ji shi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Yan kasuwa sun rage farashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa masu sayar da man fetur sun rage farashin fetur a manyan matatun ajiya da ke Legas, Warri, Fatakwal da Calabar.

Rahoto ya ce an samu saukar farashin man fetur a manyan matatun ajiya na Najeriya bayan 'yan kasuwa sun rage farashi da har N23 kan kowace lita a wasu wurare.

Kamfanin Pinnacle ya rage farashinsa da N2 zuwa N1,216 kan kowace lita, yayin da MRS ya sauke nasa zuwa N1,222 bayan rage N2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262