Sarkin Musulmi Ya Nuna Ɓacin Ransa kan Cin Zarafin Musulmai Yan Ƙabilar Igbo
- Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan kisan Kanal Abdussalam Ude
- Ya kuma yi Allah-wadai da nuna ƙiyayya da wariya ga Musulman Igbo tsiraru a Kudu maso Gabas, yana kira a tabbatar da zaman lafiya l
- Sarkin Musulmin ya ce rashin binciken kisan jami'in soja zai raunana adalci da haɗin kan ƙasa, yana roƙon Allah Ya gafarta wa mamacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya nuna damuwa kan cin zarafin yan ƙabilar Igbo Musulmi.
Mai Alfarma ya bukaci gwamnatin tarayya da rundunar sojin Najeriya su gaggauta gudanar da bincike kan kisan wani babban jami'in soja, Kanal Abdussalam Ude

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin tawagar yaɗa labaran Sarkin Musulmi, cewar Punch.
Kisan Ude: Sarkin Musulmi ya magantu
Sanarwar ta ce dole ne a gano yadda aka kashe jami'in tare da gurfanar da masu laifi a gaban shari'a.
Ya bayyana damuwa kan abin da ya kira ci gaba da nuna ƙiyayya da wariya ga Musulman Igbo tsiraru a Kudu maso Gabas. Ya ce irin waɗannan hare-hare na kawo cikas ga haɗin kan Najeriya.
Sanarwar mai taken "Sarkin Musulmi ya bukaci a fara bincike nan take kan zargin kashe wani jami'in soja Musulmin Igbo" ta ce Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne bayan rahotannin kashe babban jami'in sojan a gidansa da ke Abuja, duk da cewa daga baya aka bayyana lamarin ya faru a Nasarawa.
Ya ce gwamnati da rundunar soji dole su haɗa kai domin gano hakikanin abin da ya jawo harbe Kanal Abdussalam Ude, wanda ya bayyana a matsayin ƙwararren jami'in leƙen asirin soja da al'ummar Musulmi da gargajiya ke alfahari da shi.

Source: Twitter
Gargadin da Sarkin Musulmi ya yi
Sarkin Musulmin ya ce barin kisan ko wane ɗan Najeriya ba tare da bincike ba, musamman idan jami'in soja ne mai aiki, ba zai taimaka wajen gina ƙasa ba.
Ya jaddada cewa dole ne a gano musabbabin kisan tare da hukunta waɗanda suka aikata hakan, cewar Daily Post.
Ya kuma bukaci a kawo ƙarshen kalaman ƙiyayya da hare-hare kan tsirarun mabiya addinai a sassan ƙasar nan.
Ya ce Musulmai za su ci gaba da nuna soyayya, haƙuri, zaman lafiya da juriya kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
Sarkin Musulmin ya yi addu'ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan Ya ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe Kanal Abdussalam Ude ne yayin wani yunƙurin sace shi a gidansa da ke Badna, ƙaramar hukumar New Karu a Nasarawa, bayan ya yi ƙoƙarin kare kansa daga maharan.
'Mahaddaci ne': Tarihin rayuwar marigayi Kanal Ude
An ji cewa masu amfani da kafofin sadarwa sun bayyana rasuwar Kanal Abdulsalam Ude na DIA a Abuja a matsayin babban rashi.
Uthman Isa Tochukwu ya ce marigayin ya haddace Alkur'ani gaba ɗaya, ya kware a harshen Larabci, kuma yana cikin jami'an leken asiri.
Masu alhini sun ce rasuwarsa babban rashi ne ga Musulman Igbo da Najeriya baki ɗaya, tare da yi masa addu'ar Allah Ya gafarta masa.
Asali: Legit.ng


