Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce bincike ya nuna wasu mutum 17 na da hannu a kisan Malama Ummulkhairi kuma tuni aka gurfanar da su a gaban kotu.
Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce bincike ya nuna wasu mutum 17 na da hannu a kisan Malama Ummulkhairi kuma tuni aka gurfanar da su a gaban kotu.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara. 'Yan bindigan sun kashe jami'in tsaro tare da yin awon gaba da mutane masu yawa.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar dan daba Baba Beru bayan an harbe shi da bindiga. An harbi Beru ne yayin da 'yan daba suka kai hari.
Gwamnatin Kano ta biya N21bn daga cikin Naira biliyan 48.6 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hana wasu daga cikin 'yan fansho da suka hidimtawa jihar.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya jajantawa mutanen Benue kan hare-haren 'yan bindiga. Ya ce gwamnatin tarayya za ta dauki mataki.
Jihar Rivers ce ke da mafi yawan masu dauke da HIV a Najeriya da mutane 208,767, yayin da jimillar masu dauke da cutar a fadin kasa ya kai miliyan biyu.
Fadar shugaban kasa ta yi martani kan shirin saka wutar sola a Aso Villa da Bola Tinubu ke yi. Ta ce ko a fadar shugaban Amurka ma ana aiki da wutar sola.
Shugaban hafsoshin tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa za su tarkata dukkanin karfinsu a waje guda wajen tabbatar da kawo karshen ta'addanci.
Gwamnan Binuwai ya bayyana cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu yankuna a jihar, inda suke ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa suna salwantar da rayuka.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano, sun yi arangama da wani hatsabibin dan daba mai suna Baba Beru. 'Yan sandan sun aika da shi barzahu bayan fafatawa.
Labarai
Samu kari