Ummulkhairi: Sheikh Rijiyar Lemo Ya Yi Magana Mai Zafi kuma Ya Bukaci a Binciki DPO
- Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya yi Allah-wadai da yadda aka kashe wata malama mai suna Ummulkhairi saboda zargin bogi
- Babban malamin hadisin ya ja hankali a kan illar daukar doka a hannu, sannan ya bukaci a binciki DPO da ake zargi da mika matar
- Bayan wannan tsokaci ne sai malamin hadisin ya cigaba da gabatar da tafsirisa a cikin sura ta uku a cikin Kur’ani wato Ali-Imran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Kashe wata malamar islamiyya da aka yi a garin Marabas Jos a makon da ya gabata yana cigaba da daukar hankalin mutane.
Malaman addini sun yi magana game da mutuwar Ummulkhairi, wanda aka aika ta barzahu saboda zargin satar yara da bai tabbata ba.

Source: Facebook
Sani Umar R/Lemo ya yi maganar Ummulkhairi
A huduba da tafsirinsa na ranar Juma’a, 11 ga watan Muharram 1448 da mu ka saurara a Facebook, Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya tabo zancen mutuwar.
Farfesan na ilmin hadisi ya yi tir da wannan kisan gilla da aka yi, ya ce addinin Musulunci bai taba goyon bayan mutum ya dauki doka a hannu ba.
An ji Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya yi magana mai zafi kafin ya soma gabatar da tafirin da aka saba a duk mako a masallacin Gadon Kaya.
Al’amari ne wanda ya tayar da mutane da-dama hankali, duk wani mai tausayi ya tausaya wa wannan baiwar Allah musamman ‘yanuwanta.
Abin takaici ne a ce wannan ya faru cikin al’umma irinta tamu ta Musulmi. Har kullum muna fada, duk abin da Musulunci ya zo da shi, shi ne maslaha.
- Dr. Sani Rijiyar Lemo
Matsayar Musulunci a kan daukar doka a hannu
Muddin aka bar mutane su yi yadda suka ga dama, musamman da jahilai, masu zaman banza da ‘yan shaye-shaye suka yawaita, ya ce za a rasa rayuka.
"Shari’ar Musulunci ba ta yarda wani ya dauki doka a hannunsa ba. Mun sha fadan wannan a wurare da dama.
"Ko da mutumin ya cancaci hukuncin, kotu ta zartar da wannan hukunci, ba a zatarwa ba ta hanyar da ba alkali ba, ba hukuma ba.
- Dr. Sani Rijiyar Lemo
Babban malamin ya kara da cewa shugaba ko wakilin shugaban ne yake zartar da haddi a shari’ar Musulunci tun zamanin Annabi Muhammad SAW.
Sani Rijiyar Lemo ya ce a binciki DPO
Sani Rijiyar Lemo OON ya kuma yi tir da yadda aka ji cewa babban jami’in ‘yan sanda ne ya damka marigayiyar a hannun mutanen da suka kashe ta.
"Abin da ya kara tayar wa da mutane hankali shi ne rahotannin da aka samu da shaidun gani da ido da suka wuce shi DPO ya dauki matar nan ya mika wa mutanen gari su kashe ta.
A ce wanda aka ba alhakin kula da rayuwan mutane shi ne zai yi wannan aika-aika, ina kuma mutane za su kubuta, idan da shi za a iya wannan ta’addancin.
- Dr. Sani Rijiyar Lemo
Ganin ba a ga DPO na Marabar Jos cikin wadanda aka gurfanar ba, Rijiyar Lemo ya ce akwai sauran rina a kaba.
Shehin yake cewa damka wannan mata a kashe ta da sunan kubutar da ofishin ‘yan sanda ko wani bayani makamancin hakan ba zai zama uzuri a shari’a ba.
Karatun ya yi bayanin yadda musulunci ya fifita ran mu’umini a kan ka’aba, balle ofishin ‘yan sanda. An tsakuro bangaren fadakawar kuma an wallafa a shafin Facebook.
Legit Hausa ta fahimci darasin da aka yi a masallacin da ke Gadon Kaya a Kano shi ne na biyu tun bayan hutun bayyan sallar idi da aka tafi a watan jiya.
Amnesty ta shiga zancen mutuwar Ummulkhairi
A makon nan ne rahoto ya zo cewa kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nuna takaicinta kan kisan da aka yi wa wata malamar Islamiyya.
Wata sanarwa da aka fitar ta nuna Amnesty International ta bukaci a gudanar da sahihin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru game da kisan malamar.
Kamar yadda aka ji kungiyar ta nuna damuwa kuma kan yadda ake kara samun karuwar yawaitar kisan mutane ta hanyar daukar doka a hannu a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


