Zaben Gwamna: 'Yan Daba Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Harbi Wani Jigon APC a Osun
- Wasu mahara da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbi wani ’dan jam'iyyar APC, Taofeek Mustapha a jihar Osun
- Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da samun rigingimun siyasa gabanin zaben gwamnam jihar Osun da za a yi a watan Agusta, 2026
- Jigon APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka kawo hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Wani mamban jam’iyyar APC, Taofeek Mustapha, ya samu raunuka bayan wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbe shi a ranar Asabar a jihar Osun.
Lamarin ya faru ne a yankin Oluode-Aranyin, inda wani mazaunin yankin, Sola Hammed, ya ce maharan sun iso cikin wata mota kirar Toyota Sienna mai ruwan kasa ba tare da lambar rajista ba, sannan suka fara harbe-harbe.

Source: Original
A cewarsa, harbin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, wanda ya sa kowa ya rika neman mafaka domin kauce wa harsasan bindiga, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
“Kowa ya ruga yana neman inda zai tsira saboda gudun kada harsashi ya same shi. Daga baya muka ji wani yana neman taimako, amma a lokacin babu wanda ya kuskura ya waiwayo,” in ji Hammed.
Mamban APC ya fadi abin da ya faru
Jigon APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka fara harbin.
Ya bayyana cewa yayin da yake gudu domin ceton ransa, maharan suka bi shi saboda sun ga hular APC da ke kansa, kafin daga bisani suka harbe shi a ƙafarsa.
“Ina sanye da hular AMBO lokacin da aka fara harbin. Kowa ya gudu yana neman mafaka, amma suka biyo ni saboda hular APC da nake sanye da ita.
"Ban tsaya ba, amma suka harbe ni a ƙafa. Na yi ta neman taimako kafin daga bisani suka koma cikin motarsu suka tsere,” in ji shi.

Source: Getty Images
'Yan sanda sun fara bincike
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kai harin da dalilin faruwar lamarin.
Rahotanni na nuna cewa tashe-tashen hankula masu alaƙa da siyasa na ƙara ƙamari a jihar Osun yayin da ake shirin gudanar da zaɓen gwamna a ranar 15 ga watan Agusta, 2026.
An kuma samu rahotannin kashe-kashe a wasu sassan jihar sakamakon rikicin siyasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Mota ta murkushe masu kamfen APC
A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar wani dan APC bayan wata babbar mota ta burma cikin jerin masu kamfen na jam'iyyar a Osun.
An shirya gangamin ne domin mara wa ɗan takarar APC na gwamnan jihar Osun baya a zaɓen ranar 15 ga Agustan 2026, Bola Oyebamiji, a.garin Ede
Mutum ɗaya mai suna AbdulRasaq Ahmed ya rasa ransa, yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata bayan babbar motar ta fada kan mahalarta taron.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

