'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Zamfara, Sun Kashe Jami'in Tsaro, An Sace Mutane da Dama
- Ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙananan hukumomi guda uku na jihar Zamfara a cikin 'yan kwanakin nan
- Miyagun ƴan bindigan sun kashe mutane tare da yin awon gaba da wasu Bayin Allah masu yawa zuwa wurin da ba a sani ba
- Ƴan bindigan sun kuma kashe wani 'dan rundunar Askawaran Zamfara, aka sace abokin aikinsa bayan sun tare motarsu a hanya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da jerin hare-haren da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai a ƙananan hukumomin Zurmi, Tsafe, da Talata Mafara.
Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a ranar Talata, 22 ga watan Afrilu, waɗanda suka haifar da asarar rayuka da kuma sace mutane.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai farmaki a ƙauyen Kaiwa Namba da misalin ƙarfe 5:30 na asubahi, suka kashe wasu mazauna ƙauyen.
Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba, zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.
Haka zalika, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, wasu ƴan bindiga da ke kan babura sama da 100 sun kai hari a ƙauyen Bawa Ganga.
Jami’an ƴan sanda na rundunar Mobile Force (PMF) da ke karkashin atisayen “Restore Peace” sun daƙile harin a yayin da suka yi musayar wuta da maharan.
Wani jami’in ƴan sanda mai suna Sufeto Sunday Joel daga MOPOL 10 Bauchi ya jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma an garzaya da shi asibiti domin jinya.
An tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin, kuma an tabbatar da dawo da zaman lafiya.
Miyagun yan bindiga sun kashe jami'in tsaro
A wani harin na daban kuma da misalin ƙarfe 9:00 na safe, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan wata motar Golf da ke tafiya tsakanin ƙauyukan Bobo da Tashar Rogo a kan hanyar Anka zuwa Mayanchi.
A wannan harin, ƴan bindigan sun harbe Murtala Hali, mamba a rundunar Askarawan Zamfara da direban motar, Danjuma Abubakar.

Asali: Original
Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wani mamba na rundunar Askarawan Zamfara mai suna Bashir Kolabe.
Waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyar zuwa Gusau ne domin halartar shari’ar da ta shafi laifuffukan ƴan bindiga.
An tura dakarun hadin gwiwa na tsaro zuwa wuraren da abin ya shafa domin dawo da doka da oda da kuma hana faruwar wani harin a nan gaba.
Ƴan bindiga sun kai hari a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wau ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu ƙananan hukumomi biyu na jihar Kwara.
Ƴan bindigan sun kashe mutane shida bayan sun buɗe musu wuta a wani wurin shaƙatawa da ke cikin wata tashar mota.
Ana zargin yan bindigan sun kuma kashe wani mamba na ƙungiyar ƴan sa-kai bayan sun yi musayar wuta a cikin daji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng