'Yan Sanda Sun Kawo karshen Hatsabibin 'Dan Daba a Kano
- Jami'an ƴan sanda a jihar Kano sun kawo ƙarshen ayyukan ta'addancin wani tantirin ɗan daba da ake kira Baba Beru
- Ƴan sandan sun hallaka Baba Beru ne bayan ya yi yunƙurin farmakarsu da wuƙa lokacin da suke je kama shi a jihar Kano
- Baba Beru dai ya gamu da ajalinsa ne a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025 a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jami'an ƴan sanda a jihar Kano sun hallaka wani shahararren ɗan daba kuma wanda ake zargi da aikata fashi da makami, wanda aka fi sani da Baba Beru.
Baba Beru ya rasa ransa ne a ranar Talata bayan ya yi yunƙurin kai hari kan jami’an ƴan sanda a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan sanda suka kashe ɗan daban a Kano
Rahotanni daga ganau da majiyoyin tsaro sun nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da wasu jami’an ƴan sanda ke gudanar da sintiri na yau da kullum, suka yi arangama da Baba Beru.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa lokacin da ƴan sanda suka nemi kama Baba Beru, sai ya fusata, ya fito da wuƙa ya nufi jami’an da niyyar kai musu hari.
Wannan mataki nasa ya tilastawa jami’an su ɗauki matakin kare kai ta hanyar amfani da ƙarfi.
A nan take suka harbe shi, kuma hakan ya kawo ƙarshen firgici da fargaba da mazauna yankin ke fama da shi sakamakon aikata laifuka da ke da nasaba da marigayin.
Baba Beru ya yi suna a Kano wajen daba
Rahotanni sun bayyana cewa Baba Beru ya shahara wajen addabar jama’a da fashi da makami, satar wayoyi da kaddarorin mutane da kuma kai hari kan mazauna unguwar musamman a lokacin dare.
Har ila yau, an ce yana jagorantar wasu ƴan daba da ke cin karensu babu babbaka a cikin Kano.

Asali: Original
Kashe Baba Beru ya sanya mutane farin ciki
Bayan kisan nasa, jama’ar yankin Gwammaja sun yi murna da farin ciki, suna bayyana jin daɗinsu bisa kawar da wannan barazana ga rayuwarsu da dukiyoyinsu.
Wasu ma sun ce sun fi shekara biyu suna rayuwa cikin tsoro da damuwa saboda aikata laifukan da Baba Beru da muƙarrabansa ke yi.
Shugabannin al’umma sun yaba wa ƴan sanda bisa wannan nasara, inda suka roƙi gwamnati da ta ƙara ɗaukar matakan tsaro domin kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ƴan sandan jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.
Ƴan daba sun kashe wani mutum a masallaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan daba sun kutsa cikin masallaci yayin da ake tsaka da gudanar da sallar dare a jihar Kaduna.
Harin da ƴan daban suka kai a cikin masallacin ya yi sanadiyyar rasuwar mutum ɗaya bayan sun caka masa wuƙa.
Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, sun cafke mutum 12 da ake zargi da hannunsu a harin da aka kai kan masallatan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng