Baba Beru: An Harbe Dan Daban da Ya Yi Gaba da Gaba da 'Yan Sanda a Kano
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani sanannen dan daba mai suna Halifa Baba-Beru, bayan wata arangama da jami’anta a Gwammaja
- An kama Baba-Beru ne da rana a yankin Dala, amma 'yan daba sun kai farmaki domin ceto shi, inda hakan ya janyo musayar wuta tsakanin su da ‘yan sandan jihar
- An garzaya da dan dabar da wasu jami’an ‘yan sanda da suka ji rauni a lokacin zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa jinya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wata arangama tsakanin jami’an tsaro da wani gungun 'yan daba ta yi sanadiyyar mutuwar Halifa Baba-Beru.
Rahotanni sun bayyana cewa Baba Beru na daya daga cikin mashahuran masu aikata laifuffuka a jihar Kano.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamari ya faru ne a unguwar Gwammaja da ke karamar hukumar Dala, inda rundunar ‘yan sanda ta gudanar da samame domin cafke Baba-Beru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani babban jami’in ‘yan sanda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana, inda daga bisani abubuwa suka rikice bayan da 'yan daba suka kai hari kan motar sintirin da ta kama shi.
An tabbatar da mutuwar Baba Beru
A cewar majiyoyin ‘yan sanda, ana kama Baba-Beru wasu abokan cin mushen shi suka fito da makamai domin ƙoƙarin ceto shi daga hannun jami’an tsaro.
Musayar wuta ta biyo baya, wanda hakan ya janyo rauni ga wasu jami’ai biyu: Kofur Abdullahi Ibrahim da Sajan Yahaya Sa’idu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa haka ya sanya dan daba Baba-Beru samu rauni sakamakon harbin bindiga.
Dukkan su ukun an garzaya da su Asibitin Murtala Mohammed domin ba su kulawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwar Baba-Beru a yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa.

Asali: Facebook
'Yan sanda za su cigaba da yakar 'yan ta'adda
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ana cigaba da bincike a kan lamarin, kuma an ƙaddamar da farautar sauran miyagun da suka tsere daga wurin da abin ya faru.
Jami'an rundunar sun bayyana cewa jami’an tsaro ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaron al’umma da kawar da masu tada zaune tsaye a sassa daban-daban na jihar.
Haka kuma rundunar ta bukaci al’umma su ci gaba da ba da hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama 'yan dabar da suka ɓuya.
'Yan kungiyar Mahmuda sun zafafa kai hari
A wani rahoton, kun ji cewa sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta Mahmuda ta fara zafafa hare hare a yankunan Arewa ta Tsakiya.
Biyo bayan bayyanar 'yan ta'addan, gwamnan jihar Kwara ya ziyarci wata karamar hukumar da ake cewa suna kai hare hare domin daukar matakin da ya dace.
Wasu na alakanta 'yan ta'addan da bangaren Boko Haram da Abubakar Shekau ya jagoranta yayin da 'yan sandan jihar suka musanta samuwar su.
Asali: Legit.ng