Matsalolin da Ke Jawo Sabani tsakanin Shugabannin Amurka da Isra'ila a Tarihi
Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi wa Iran ta fuskanci tsananin adawa daga Isra'ila.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Lebanon, abin da ake ganin ya saɓa wa yarjejeniyar da Donald Trump da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, suka sanya wa hannu a hukumance.

Source: UGC
Sabanin da aka samu tsakanin Isra'ila da Amurka
Rahoton Al Jazeera ya bayyana cewa ana yawan samun sabani tsakanin shugabannin Amurka da Isra'ila tun shekarun baya.
Majiyoyi da dama sun nuna cewa akwai saɓani tsakanin shugabannin Amurka da na Isra'ila.
Sai dai irin waɗannan rahotanni ba su taɓa raunana goyon bayan da Amurka ke bai wa ƙawarta ta kut-da-kut ba.

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
Legit Hausa ta duba muku matsalolin da ke jawo sabani tsakanin shugabannin kasashen biyu.
1. Hadin kan Isra'ila da Faransa, Birtaniya (1956)
Wasu na ganin rikicin da ya fi muni tsakanin Amurka da Isra’ila ya faru ne a lokacin Rikicin Suez, cewar Time Magazine.
Isra’ila ta haɗa kai da Birtaniya da Faransa wajen kai hari kan Masar bayan gwamnatin Alkahira ta ƙwace ikon Mashigar Suez (Suez Canal), lamarin da ya fusata shugaban Amurka na lokacin, Dwight Eisenhower.
Washington ta ji tsoron cewa yaƙin zai ƙara ƙarfin tasirin Tarayyar Soviet a duniyar Larabawa, inda Eisenhower ya fito fili ya buƙaci firaministan Isra’ila na lokacin, David Ben-Gurion, ya janye sojojin Isra’ila.
Rahotanni sun ce har ya yi barazanar matsin tattalin arziki da na diflomasiyya. Daga ƙarshe, Masar ta ci gaba da riƙe ikon mashigar ruwan.

Source: UGC
2. Mamayar Isra'ila a yankin Falasdinu a (1991)
Bayan Gulf War, shugaban Amurka na lokacin, George H. W. Bush, ya yi kokarin samar da tattaunawar sulhu tsakanin Larabawa da Isra’ila, tare da nuna adawa da fadada matsugunan Yahudawa a yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye.
Gwamnatin Bush ta dakatar da lamunin dala biliyan 10 da firaministan Isra’ila na lokacin, Yitzhak Shamir, ya nema, har sai Isra’ila ta magance damuwar da ake da ita kan fadada matsugunan Yahudawa, cewar rahoton MERIP.
Wannan ya haifar da sabani a bainar jama’a, inda Bush ya yi fice da kalamansa cewa shi “ƙaramin mutum guda ne da ke shi kaɗai” a Capitol Hill, yana mayar da martani ga kokarin kungiyoyin masu goyon bayan Isra’ila na matsa masa lamba.
Sai dai wannan matakin bai haifar da raguwar taimakon Amurka ga Isra’ila sosai ba, kuma dangantakar soji tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da ƙarfafa.
3. Nuna iko tsakanin Netanyahu da Clinton (1996)
Kusan wata guda kacal bayan hawansa mulki a karon farko a shekarar 1996, Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka na lokacin, Bill Clinton, a Washington. Sai dai ganawar ba ta tafi yadda ake fata ba.
Rahotanni sun ce bayan ganawar, Clinton ya tambayi masu taimaka masa cewa: “Wane ne yake tsammanin shi? Wace kasa ce mai karfin iko a nan?”
Yayin da Clinton ya shiga mulki yana goyon bayan yarjejeniyar Oslo Accords da aka fara a zamanin tsohon firaministan Isra’ila, Yitzhak Rabin, Netanyahu ya nuna adawa da sharadin yarjejeniyar da ke bukatar dakatar da gina matsugunan Yahudawa.
Daga baya Netanyahu ya yi ikirarin yadda ya yi nasarar raunana tsarin yarjejeniyar Oslo. Yawan Yahudawan da ke zaune a matsugunan da ake takaddama a kansu ya karu daga kusan mutum 250,000 a shekarun 1990 zuwa kusan 700,000 a yau, Times of Israel ta ruwaito.
Yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawa mai tsanani tsakanin Netanyahu da shugaban Falasdinawa na lokacin, Yasser Arafat.
A watan Mayun shekara ta gaba, gwamnatin hadakar da Netanyahu ke jagoranta ta rushe, kuma Ehud Barak ya karbi mukamin firaministan Isra’ila.

Source: UGC
4. Rikicin Obama da Netanyahu kan nukuliyar Iran
Wannan shi ne watakila rikicin da ya fi bayyana a bainar jama'a tsakanin Amurka da Isra'ila cikin shekarun baya-bayan nan.
Dangantakar tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ta fara lalacewa ne kan gina matsugunan Yahudawa a Gabar Yamma da aka mamaye, sannan daga baya kan tattaunawar gwamnatin Amurka da Iran game da shirinta na nukiliya.
Rikicin ya kai kololuwa a shekarar 2015 lokacin da Netanyahu ya amince da gayyatar 'yan jam'iyyar Republican domin ya yi jawabi a gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda ya soki manufofin Obama kan Iran.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa yarjejeniyar nukiliyar da ake shirin kulla wa "za ta share wa Iran hanya zuwa mallakar bam din nukiliya", cewar The World Street Journal.
Tsagaita wuta: Isra'ila ta bijire wa Amurka
An ji cewa Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi magana game da yarjejeniyar Amurka da Iran a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Katz ya bayyana cewa Isra’ila ta sanar da matsayinta karara cewa ba za ta janye dakarunta ba, yana mai kiran hakan nasarar diflomasiyya.
Ya ce shugabannin Isra’ila sun fadawa jami’an Amurka cewa kasancewar sojoji a yankin na da muhimmanci wajen kare mazauna arewacin kasar.
Asali: Legit.ng


