An Kama Shugabannin 'Yan Ta'adda 7 a Filin Jirgin Sama bayan Sun Dawo daga Hajji

An Kama Shugabannin 'Yan Ta'adda 7 a Filin Jirgin Sama bayan Sun Dawo daga Hajji

  • Hukumomin tsaro sun cafke wasu da ake zargi kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne guda bakwai bayan dawowarsu daga aikin Hajji
  • Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a filin jirgin saman Katsina lokacin da suka dawo daga Saudiyya
  • Ministan ya danganta nasarar kamen da ingantaccen tsarin tantance bayanan sirri da hada bayanan NIMC da sauran hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumomin tsaro sun kama mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne bayan dawowarsu daga aikin Hajji na shekarar 2026.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An cafke wasu da ake zargin shugabannin 'yan ta'adda ne a filin jirgin saman Katsina
Taswirar jihar Katsina, inda aka kama wasu shugabannin 'yan ta'adda 7. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tunji-Ojo ya fadi hakan ne jim kadan bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar hukumar tantance bayanan 'yan kasa (NIMC) ta 2026, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: 'Yan daba sun buɗe wa mutane wuta, sun harbi wani jigon APC a Osun

An cafke 'yan ta'adda a filin jirgin Katsina

A cewar ministan, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis din makon jiya a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan sun dawo daga Makka.

Mr. Olubunmi Tunji-Ojo ya ce an mika wadanda aka kaman ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin ci gaba da gudanar da bincike.

Tunji-Ojo ya ce:

“Na yi farin cikin sanar da cewa a ranar Alhamis din makon jiya, an kama bakwai daga cikin sanannun kwamandojin Boko Haram da ISWAP yayin da suke dawowa daga Makka a filin jirgin Katsina, sannan aka mika su ga DSS.”

Ba a fadi sunayen wadanda aka kama ba

Sai dai ministan bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, ko kuma ko sun kasance cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke nema kafin tafiyarsu zuwa Saudiyya.

Haka kuma bai bayyana yadda suka samu izinin tafiya ba ko kuma ko an riga an gurfanar da su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe shugaban Fulani na kungiyar Miyetti Allah

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga DSS ko Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) kan kamen ba.

Ministan harkokin cikin gida Tunji-Ojo ya yi bayanin yadda aka kama shugaannin 'yan ta'adda 7 a Katsina
Ministan harkokin cikin gida Tunji-Ojo ya na jawabi a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: @BTOofficial
Source: Twitter

Fasaha ta taimaka wajen gano su

Ministan ya danganta nasarar kamen da ingantaccen tsarin hada bayanan shaida na kasa da kuma tsarin kula da iyakokin Najeriya kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce bayanan Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) yanzu suna hade da bayanan shige da fice da kuma wasu hanyoyin sadarwa na tsaro na kasa da kasa.

A cewarsa:

“Wannan ya yiwu ne saboda bayanan NIMC sun hade da bayanan shige da fice, kuma suna aiki tare da tsarin Interpol na sa’o’i 24.”

Tunji-Ojo ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji tsarin kula da bayanan mutane da ba su hade ba, wanda hakan ke kawo matsala wajen musayar bayanai tsakanin hukumomi.

Sojoji sun matsawa 'yan Boko Haram

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun sojojin Najeriya sun matsawa 'yan ta'addan Boko Haram da kai hare-hare ta sama da kasa a maboyarsu da ke Borno.

Matsin lambar da aka yi wa 'yan ta'addan ya sanya an samu nasarar ceto mutanen da suke tsare a hannunsu a cikin daji,

Rundunar sojoji ta bayyana cewa za ta ci gaba da matsa lamba ga 'yan ta'adda har sai an tabbatar da fatattakarsu daga yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com