An Rasa PDP da ADC a Gombe da APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi

An Rasa PDP da ADC a Gombe da APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi

  • Hukumar zabe mai zaman kanta a Gombe, GOSIEC ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi APC
  • An gudanar da zaben ne a yau Asabar 27 ga watan Yunin 2026 na kujerun shugabannin kananan hukumomi 24 da kujerun kansiloli 240
  • Wani masoyin Farfesa Isa Ali Pantami kuma ɗan jam'iyyar PDP, Mohammed Babayo Pantami ya yi fatali da maganar gudanar da zaben kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Gombe (GOSIEC) ta bayyana sakamakon zabukan kananan hukumomi da na kansiloli a jihar.

Hukumar ta ayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 24 da kuma kujerun kansiloli 240.

APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganawa da manema labarai a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Twitter

Sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kotun Najeriya ta yanke wa Ibrahim da Abdullahi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Yawa jam'iyyun da suka fafata a zaben Gombe

Jam'iyyu shida ne suka tsayar da 'yan takara a zaben shugabannin kananan hukumomi, ciki har da APC, Youth Party, NRM, ZLP, AAC da DLA.

An gudanar da zaben a gundumomi 114 da rumfunan zabe 2,988, inda masu kada kuri'a suka zabi shugabannin kananan hukumomi da kansiloli cikin yanayi da masu sa ido suka bayyana a matsayin lumana.

An fafata a kujerun shugabannin kananan hukumomi 11 da kuma sababbin yankunan ci gaban kananan hukumomi 13, wanda ya kawo adadin kujerun shugabanni zuwa 24 gaba daya.

A lokaci guda kuma, an zabi kansiloli 240 domin wakiltar gundumominsu a fadin jihar, bayan an gudanar da kada kuri'a cikin tsari.

Gwamna Inuwa ya yabawa al'ummar Gombe kan fitowa zabe
Taswirar jihar Gombe da aka gudanar da zaben kananan hukumomi. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni sun nuna cewa an samu fitowar masu kada kuri'a a al'ummomi da dama, lamarin da ya nuna karuwar sha'awar jama'a kan mulkin kananan hukumomi.

Martanin Gwamna Inuwa game da zaben

Gwamna Inuwa Yahaya ya kada kuri'arsa a rumfar Yahaya Umaru da ke Gombe, inda ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana.

Kara karanta wannan

Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta shigo Arewacin Najeriya? 'Yan sanda sun gano gaskiya

Ya ce yanayin zaman lafiyar da aka samu ya nuna balaga ta masu kada kuri'a da kuma jajircewar masu ruwa da tsaki wajen kare dimokuradiyya.

Gwamnan ya kuma bukaci dukkan jam'iyyun siyasa da 'yan takara su amince da sakamakon zaben cikin aminci, tare da fifita ci gaban Gombe da dimokuradiyya fiye da bukatun jam'iyya.

Wani masoyin Pantami ya zanta da Legit Hausa

Mohammed Babayo Pantami ya yi fatali da maganar gudanar da zaben kananan hukumomi a Gombe.

Ya ce zaben je ka na yi ka ne kawai saboda mutane da dama ba su ma san ana zaben ba.

Ya ce:

"A matsayina na ɗan PDP, masoyin Farfesa Isa Ali Pantami wannan zaɓe na kananan hukummomi da kansiloli da akace anyi yau a Jihar Gombe zabe ne na jeka na yi ka ne.
"Yawancin al’umma ma ba su san ana gudanar da shi ba, wannan shi ya nuna yadda jam'iyyar APC mai ci ta yi amfani da karfin ta wajen takaita bawa manyan jam’iyyun adawa damar shiga wannan zabe."

Pantami: An kori Gombawa Motors daga tashar gwamnati

Kara karanta wannan

Jerin kujerun da APC ta lashe a zaben ranar 20 Yunin 2026

Mun ba ku labarin cewa hukumomi sun umarci kamfanin sufuri na Gombawa Motors ya fice daga tashar mota ta Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park cikin sa’o’i 24.

Matakin ya zo ne kwanaki biyu bayan kamfanin ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.

Mahukuntan Mega Park sun ce korar ta samo asali ne daga zargin karya ƙa’idojin aiki da koke-koken masu sufuri, ba saboda siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.