Ran Tinubu Ya Ɓaci kan Kashe Kashe, an Ji Me Ya Faɗawa Ribadu da Shugabannin Tsaro

Ran Tinubu Ya Ɓaci kan Kashe Kashe, an Ji Me Ya Faɗawa Ribadu da Shugabannin Tsaro

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su sauya dabarunsu nan take domin kawo karshen tashin hankali a Borno, Benue da Plateau
  • Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro na tsawon sa'o’i biyu a Abuja, inda ya ce kashe fararen hula da ake yi a jihohin nan ya isa haka
  • Nuhu Ribadu ya ce Tinubu ya bukaci hadin gwiwa da kananan hukumomi da gwamnonin jihohi don yakar matsalolin tsaro a kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya fusata game da kashe-kashe da ake yi a jihohin Plateau, Benue da Borno.

Tinubu ya umarci a sauya dabarun tsaro nan take da kuma daukar matakan gaggawa don kawo karshen tashin hankali a wasu jihohi.

Tinubu ya yi zama da Ribadu da shugabannin tsaro
Bola Tinubu ya nuna damuwa kan kashe-kashe da ake yi a Najeriya. Hoto: Nuhu Ribadu, HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ran Bola Tinubu ya ɓaci kan matsalar tsaro

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a daren yau Laraba 23 ga watan Afrilun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya gana da hafsoshin tsaro na tsawon sa’o’i biyu a fadar gwamnati, inda ya ce ya zama dole a dakatar da kashe fararen hula.

Yayin da yake tir da lamarin, Tinubu ya ce:

"Ya isa haka, abin ya isa haka."

Mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya ce hafsoshin tsaro sun ba shugaban rahoto kan hare-haren da aka kai da asarar rayuka.

Ribadu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya umarci amfani da sabuwar hanya wajen fuskantar matsalar tsaro da ke addabar kasar.

Ya ce:

"Shugaban kasa ya ba mu dama mu kara masa bayani, mun yi dogon taro, mun ba shi sabbin bayanai game da halin da ake ciki.
"A yau, mun samu dama mu sake masa bayani, kuma taron ya dauki lokaci mai tsawo. Mun saurare shi, mun karbi sababbin umarni.

"Ya ce mu kara himma wajen dawo da zaman lafiya a kasar nan. Mun shaida masa cewa mun bi umarninsa a wuraren da ake fama da matsala."
"Mun je jihohin da ake fama da rikici kamar Plateau, Benue da Borno. Mun ba shi rahoto bisa ga umarnin da ya ba mu."
Abin da Tinubu ya fadawa Ribadu da shugabannin tsaro
Tinubu ya nuna damuwa kan rashin tsaro, ya ba Ribadu da shugabannin tsaro umarni. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Abin da Tinubu ya fadawa Nuhu Ribadu

Ribadu ya ce Shugaban kasa ya jaddada bukatar hada kai da kananan hukumomi da gwamnonin jihohi wajen fuskantar matsalolin tsaro.

Ya kara da cewa:

"Matsalar tsaro ba a matakin kasa kadai take ba, kananan hukumomi da al'umma na da rawar da za su taka."
"Dole ne mu hada kai da al’umma, da kananan hukumomi da kuma gwamnonin jihohi."

Rashin tsaro a Najeriya

Duk da zuba kuɗi masu yawa da gwamnatin Tinubu ke yi don dakile rashin tsaro, matsalar na ci gaba da ta’azzara a sassa daban-daban na Najeriya.

Tun hawansa mulki, shugaban ya karɓi ƙasa da ke fama da rikice-rikice da dama — daga Boko Haram a Arewa maso Gabas, rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya, zuwa garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana takaicinsa kan yadda kashe-kashe da hare-hare ke ci gaba da faruwa, musamman a Borno, Benue da Plateau, inda ya umarci jami’an tsaro su sauya dabaru nan take.

Ya kuma bukaci haɗin gwiwa da gwamnonin jihohi da kananan hukumomi domin shawo kan matsalar.

Sai dai, duk da waɗannan matakan da gwamnati ke ɗauka, hare-haren da ke kashe fararen hula sun ƙi ci sun ƙi cinyewa.

Wannan ya haifar da tambayoyi game da tasirin kuɗaɗen da ake kashewa, da kuma gazawar tsare-tsare.

A karshe, rashin tabbataccen sauyi ya bar jama’a cikin damuwa, tare da fargabar cewa matsalar tsaro na iya ci gaba da zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

Ana zargin Fubara zai dawo APC

Kun ji cewa wasu na hasashen cewa dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara na shirin daukar wasu matakai da za su kawo karshen rikicin siyasa a Rivers.

Rahotanni sun ce Fubara, bayan ganawarsa da Bola Tinubu a London, zai iya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Shugabannin sun yi ganawar farko tun bayan ayyana dokar ta baci a Rivers, wanda wasu ke ganin gwamnan na neman sulhu ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.