"Ba Haka Buhari da Jonathan Suka Yi ba," Atiku Abubakar Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu
- Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da yunkurin maida Najeriya tsarin jam'iyya daya
- 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar ADC ya nuna damuwa kan yunkurin soke rijistar NDC ta hanyar amfani da kotu
- Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi koyi da tsofaffin shugabannin Najeriya, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi koyi da tsofaffin shugabannin kasa, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu daya daga cikin wadannan shugabanni, Buhari da Jonathan, da ya yi yunkurin soke rajistar jam’iyyun adawa duk da tsananin gasa a siyasa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan abin da ya kira yunkurin soke rajistar jam’iyyar NDC ta hanyar amfani da kotu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na son raunana jam’iyyun adawa gabanin babban zaben 2027.
Atiku ya caccaki tsarin jam'iyya daya
A cikin wata sanarwa da Ofishin Yada Labaran Atiku ya fitar ranar Asabar, Atiku ya bayyana cewa matakin da ake zargin gwamnati na dauka wani bangare ne na shirin kafa tsarin jam’iyya daya a Najeriya.
Ya ce irin wannan mataki na iya raunana dimokuraɗiyya tare da rage amincewar jama’a da tsarin gudanar da zabe.
A cewarsa, ya kamata a bai wa ’yan Najeriya damar shiga sahihin zabe tare da zabar shugabanninsu ba tare da wata katsalandan ba.
Atiku ya kafa misali da Buhari, Jonathan
Atiku ya ce abin da aka yi wa jam’iyyar NDC ya saba da alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi na kare dimokuraɗiyya.
Ya bukaci shugaban kasar ya yi koyi da marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda duk da kasancewarsa tsohon soja kuma dan siyasa, bai taba soke rajistar wata jam’iyyar adawa ba a lokacin mulkinsa.
Haka kuma ya yabawa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, yana mai cewa ya kasance yana jaddada cewa burin siyasa bai kamata ya fi darajar rayukan al’umma ba.
Ya ce:
“Idan har da gaske kana da farin jini kuma manufofinka sun inganta rayuwar al’umma, bai kamata ka ji tsoron fafatawa cikin zabe na gaskiya da adalci ba.”
Ya bukaci kotuna su kare martabarsu
Atiku ya kara da cewa shugabanni su rika kare ka’idojin dimokuraɗiyya ta hanyar bai wa jam’iyyu damar yin gogayya cikin adalci maimakon kokarin raunana su.
Ya kuma yi kira ga alkalan Najeriya da su kare ’yancin kai da mutuncin bangaren shari’a, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Source: Facebook
Ya bukace su da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da kotuna domin cimma manufofin siyasa, yana mai cewa bangaren shari’a na taka muhimmiyar rawa wajen dorewar dimokuraɗiyyar Najeriya.
ADC ga hango nasarar Atiku a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi zai ba da mamaki a zaben 2027.
ADC ta yi ikirarin cewa Atiku da Amaechi za su iy kayar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Jam'iyyar ta yi amanna cewa kowane ɗaya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta zai samar da shugabanci mafi kyau fiye da gwamnati mai ci yanzu.
Asali: Legit.ng


