Rundunar Sojin Najeriya Ta Fadi Abin da aka Shirya bayan Yawaitar Kashe Kashe

Rundunar Sojin Najeriya Ta Fadi Abin da aka Shirya bayan Yawaitar Kashe Kashe

  • Shugaban hafsoshin tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya ce rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da kare martaba da rayuka
  • Ya yi wannan jawabi ne yayin taron addu'a da aka gudanar a jihar Kaduna, a dai dai lokacin da rashin tsaro ke kara lalata sassan kasar nan
  • Rahotanni a baya-bayan nan sun bayyana cewa an samu karuwar matsalar rashin tsaro, inda aka kashe daruruwan jama'a a Binuwai da Filato
  • Mahalarta taron sun bukaci gwamnati ta tashi tsaye a magance matsalar tsaro, matsin tattalin arziki, rashin ingantaccen ilimi da lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi magana a kan tsanantar matsalar tsaro a sassan kasar nan.

Ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya za ta yi amfani da dukkannin kayan aiki da dama da take da su domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar.

Janar
Rundunar sojojin kasar nan ta ce ana shirin kawo karshen rashin tsaro Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

AIT News ta ruwaito Janar Musa ya bayyana haka ne yayin taron addu’a na musamman da aka gudanar a yankin Kudancin Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Southern Kaduna Solemn Assembly ta shirya wannan taro kwanan nan.

Rashin tsaro: Shugaban sojojin Najeriya ya magantu

Shugaban hafsoshin tsaron ya yi jawabi ga mahalarta taron, ya jaddada cewa dakarun tsaro na kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ‘yan ta’adda da kuma kare rayuwarsu.

A cewar Janar Musa:

“Sojojin Najeriya sun kuduri aniyar ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan, kuma ba za mu bari wasu su hana zaman lafiya da ci gaban kasa ba.”

Mahalarta taron addu'ar sun bukaci gwamnati a matakai daban-daban da su kara zage damtse wajen magance matsalar tsaro, da kuma sauran kalubalen da ke hana ci gaban Najeriya.

An yi addu’a saboda matsalar rashin tsaro

Taron ya hada manyan malaman addini, sarakunan gargajiya, masana da kuma wasu muhimman ‘yan kasa daga kabilun Kudu na jihar Kaduna.

Sun taru domin yin addu’o’i na musamman don neman zaman lafiya, hadin kai da kuma daidaituwar tattalin arziki, ba kawai a Kudu na Kaduna ba, har ma a fadin Najeriya baki daya.

Sojoji
Wasu daga cikin sojojin kasar nan Hoto: Nigeria Army HQ
Asali: Facebook

Sun kuma jaddada bukatar kawo karshen matsin tattalin arziki, karancin ingantaccen ilimi da kuma rashin wadataccen kula da lafiyar al’umma.

A cewarsu, wadannan matsaloli na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa tabarbarewar tsarin rayuwa a kasar.

An samu karuwar rashin tsaro

A baya, mun ruwaito cewa gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa jihar Filato ba ta taba samun cikakken tsaro tun lokacin da aka koma mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Ya ce jihar na fama da mamayar 'yan ta'adda da 'yan bindiga da suka mamaye dazuka, filayen kiwo da kuma wuraren ajiyar namun daji a sassa daban-daban na jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da aka shirya tare da fitattun ‘yan jihar da masu ruwa da tsaki, domin nazarin halin da ake ciki bayan kisan gillar da ake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.