Asiri Ya Kara Tonuwa kan Kisan Malama Ummulkhairi a Hanyar zuwa Wa'azi a Kaduna

Asiri Ya Kara Tonuwa kan Kisan Malama Ummulkhairi a Hanyar zuwa Wa'azi a Kaduna

  • Rundunar 'yan sandan Kaduna ta gano tare da kama karin mutum 17 da ake zargin suna da hannu a kisan Malama Ummulkhairi
  • 'Yan sanda sun kuma gurfanar da wasu mutum 33 kan laifin haɗa baki da kuma taron da ba bisa ka'ida ba a Marabar Jos
  • Rundunar ta ce ta saki mutum 30 da aka fara kamawa tun farko bayan bincike ya nuna ba su da hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama tare da gurfanar da karin mutum 17 a gaban kotu kan kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi a yankin Maraban Jos.

Rundunar ta bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda aka tabbatar yana da hannu a kisan.

Kara karanta wannan

Wata 'yar sanda ta jefa kanta a shari'ar N300m a Abuja, kotu ta sa a kamo ta

Yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

An gurfanar da karin waɗanda ake zargi

Tashar Channels tv ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da sababbin waɗanda ake zargin a ranar 25 ga Yunin 2026.

Ya ƙara da cewa bayan kammala binciken farko, an kuma gurfanar da wasu mutum 33 bisa zargin haɗa baki da kuma shiga taron da ba bisa ƙa'ida ba dangane da lamarin.

An saki mutum 30 bayan bincike

Rundunar ta bayyana cewa mutum 30 da aka fara kamawa kan wannan al'amari an sake su ba tare da wani sharaɗi ba, bayan bincike ya tabbatar da cewa ba su da hannu a aikata laifin.

Sanarwar ta ce:

"Bincike kan wannan lamari na ci gaba. Muna ƙara ƙaimi wajen gano da kuma kamo duk waɗanda suka aikata ko suka taimaka wajen aikata wannan mummunan laifi. Duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi a gaban shari'a."

Kara karanta wannan

An kama mota cike da takalma irin na sojoji ta nufi dajin Zamfara

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Rabiu, ya sake jaddada kudirin rundunar na tabbatar da an yi wa marigayiyar adalci tare da ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar.

Ya kuma buƙaci al'umma su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka, tare da ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa binciken.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kisan matar ya jawo ce-ce-ku-ce

Kisan Malama Ummulkhairi, malamar addinin Musulunci, ya faru ne bayan wasu sun zarge ta da satar yara a Maraban Jos, kamar yadda Punch ta kawo rahoto.

Lamarin ya jawo Allah wadai daga jami'an tsaro, ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin al'umma, waɗanda suka bayyana abin a matsayin mummunan misali na ɗaukar doka a hannu.

Matakin da shugaban yan sanda ya dauka

A wani rahoton, kun ji cewa Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Disu Tunji ya bukaci a gudanar da bincike na musamman a kan malamar Islamiyya da aka kashe a Kaduna.

Shugaban yan sandan ya kuma bada umarcin bincikar DPO na caji ofis din Mafabar Jos, wanda ake zargin ya yi sakaci har aka kashe Malama Ummulkhairi.

Matakin binciken ya biyo bayan korafi da aka mika game da zargin cewa dan sanda ne ya mika matar ga mutane suka kashe ta a Maraban Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262