Nadin Sarauta: Obasanjo, Kwankwaso, Tambuwal Sun Je fadar Sanusi II
- Jagoran NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci bikin naɗa Garkuwan Kano da Sarkin Fulanin Ja'idinawan Kano a fadar Sanusi II
- Tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya taya mutanen da aka ba sarautar murna, yana mai cewa sun dace da hakan
- Bayan Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal, taron ya samu halartar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da jami'an Abba Kabir Yusuf
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Taron nadin sarautar Garkuwan Kano da Sarkin Fulanin Ja'idinawan Kano ya tattaro manyan mutane daga ciki da wajen jihar.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na daya daga cikin manyan Najeriya da suka hallara fadar Sarki Sanusi II domin shaida nadin sarautar.

Source: Facebook
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya wallafa sakon tarya murna ga Abubakar Balarabe Mahmoud da Muhammad Dikko Umar da aka ba sarauta a Facebook.
Bayanin da Kwankwaso ya yi
Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shi ma ya hallara wajen nadin sarautar tare da dan takarar gwamnan Kano a NDC, Aminu Gwarzo.
Ya ce:
"Na samu damar halartar bikin naɗa Abubakar Balarabe Mahmoud, OON, SAN, a matsayin Garkuwan Kano.
Bikin da aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Kano, ya kuma shaida naɗa Air Marshal Muhammad Dikko Umar (mai ritaya) da sarautar Sarkin Fulanin Ja'idinawan Kano da mai martaba Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, Sarkin Kano ya yi."
Bikin ya samu halartar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, GCFR, tare da taron fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar.
Bayanin Aminu Tambuwal
Sanata Aminu Waziri Tambuwal na daya daga cikin fitattun mutanen da suka hallara wajen taron tare da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo da jami'an gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Shafin da ke yada manufofin tambuwal ya sanar da cewa:
"Sanata Aminu Waziri Tambuwal, CFR, ya haɗu da 'yan uwa, abokai, abokan hulɗa da sauransu a fadar mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II domin shaida bikin naɗa wasu fitattun 'yan Najeriya biyu da manyan sarautu.
"Bikin ya shaida naɗa fitaccen lauya kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Abubakar Balarabe Mahmoud, SAN, da sarautar Garkuwan Kano, yayin da aka nada tsohon babban hafsan sojin sama, Air Marshal Muhammad Dikko Umar (mai ritaya), Sarkin Fulanin Ja'idinawan Kano."
Sanata Tambuwal ya bayyana sarautun a matsayin karramawa da ta dace ga fitattun 'yan Najeriya biyu waɗanda gudunmawarsu ga ci gaban ƙasa da kuma hidimar da suka yi a fannonin aikinsu suka sa suke samun girmamawa da yabo."

Source: Facebook
Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya kuma yaba wa mai martaba sarki Muhammadu Sanusi II bisa ci gaba da raya kyakkyawar al'adar karrama masu nagarta da gaskiya.
Sanusi ya ba ECOWAS shawara
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da sauran kasashen ECOWAS.
Ya bukaci shugabannin ECOWAS da su sake nazari kan ficewar wasu kasashe daga kungiyar da ke kokarin hada kan yankin a fannoni da dama.
Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun sanar da fita daga kungiyar ECOWAS ne bayan sojoji sun kifar da gwamnatocin farar hula.
Asali: Legit.ng

