An Sauke Wasu Manyan Sojojin Najeriya, an Nada Sababbin Kwamandoji
- Rahoto ya nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta yi gagarumin sauyi a muƙaman manyan hafsoshinta domin ƙarfafa tsaro a fadin kasar
- An sanar da cewa sauye-sauyen sun shafi kwamandojin rundunoni, shugabannin makarantu da manyan jami'an gudanarwa a wurare
- Sojoji sun nada sababbin Janarori da kwamandoji domin jagorantar wasu rundunoni na musamman da cibiyoyin horaswa a faɗin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da gagarumin sauyin muƙaman manyan hafsoshinta, inda aka yi canje-canje a muhimman muƙaman gudanar da ayyuka, jagoranci, horaswa da gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da saraktar hulɗa da jama'a ta rundunar mai riƙon ƙwarya, Kanal Appolonia Anele, ta fitar, an bayyana cewa an yi sauyin ne a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma inganta tasirin ayyukan soji.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ƙara da cewa sauye-sauyen sun shafi kwamandojin da ke fagen daga, shugabannin makarantu da kuma manyan jami'an gudanarwa a Hedikwatar Soji.
Ta ce babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya amince da wannan tsarin sauya wuraren aiki na manyan hafsoshin, yana mai cewa matakin na da nufin ƙara wa rundunar ƙarfi wajen fuskantar sababbin ƙalubalen tsaro.
Sauye-sauyen da sojoji suka yi
An naɗa Manjo Janar WM Dangana a matsayin Babban Kwamandan Runduna ta 3 ta Sojin Najeriya (GOC) kuma Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Endurin Peace, inda zai maye gurbin Manjo Janar EF Oyinlola.
Hakazalika, an naɗa Manjo Janar EI Okoro a matsayin Babban Kwamandan Runduna ta 6 ta Sojin Najeriya da kuma Kwamandan Bangaren Ƙasa na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Safe Delta, inda zai maye gurbin Manjo Janar EE Emeka.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an naɗa Manjo Janar JR Lar a matsayin Kwamandan Hedikwatar Garrison ta Soji, yayin da Birgediya Janar OM Oyekola zai yi aiki a matsayin Sakataren Soji mai riƙon ƙwarya.

Kara karanta wannan
NADCEL: An gano sabuwar hanyar da ake damfarar ƴan Najeriya da sunan rundunar soji
Karin sauye-sauyen sojoji
A wani mataki na ƙarfafa jagoranci da shirye-shiryen yaƙi, an naɗa Birgediya Janar IB Buhari a matsayin Kwamandan Hedikwatar Birgediya ta 63, yayin da Birgediya Janar K Rabiu ya zama Kwamandan Hedikwatar Birgediyar Artilari ta 31.
A wani sauyi da ke nuna yadda rundunar ke ƙara mai da hankali kan fasaha da sababbin barazanar tsaro, an naɗa Manjo Janar SA Emmanuel a matsayin Kwamandan Rundunar Sararin Samaniya ta Sojin Najeriya.

Source: Facebook
PM News ta wallafa cewa n kuma naɗa Manjo Janar O Adegbe a matsayin Daraktan Leken Asiri da Tsaro a Hedikwatar Tsaro.
Sauyi a makarantun soji
A fannin ilimi da bunƙasa cibiyoyi, an naɗa Manjo Janar KE Chigbu a matsayin Mataimakin Kwamandan Kwalejin Tsaro ta Ƙasa, yayin da Manjo Janar SD Makolo ya zama Kwamandan Makarantar Sulke ta Sojin Najeriya.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Manjo Janar SO Adejimi a matsayin Kwamandan Makarantar Sufuri ta Sojin Najeriya, da Manjo Janar FS Etim a matsayin Babban Jami'in Horaswa a Hedikwatar Rundunar Horaswa da Koyarwa ta Sojin Najeriya (TRADOC).
An kuma naɗa Birgediya Janar U Ahmad a matsayin Kwamandan Depot na Sojin Najeriya da ke Zariya a jihar Kaduna.
Sauyin ya kuma haɗa da naɗa Manjo Janar KO Ukandu a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa na Kamfanin PHDL, yayin da aka naɗa Manjo Janar AI Allison a matsayin Manajan DPL.
Sojoji sun kai farmaki Filato
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai wani gagarumin farmaki kan masu garkuwa da mutane a wasu yankunan Filato.
Bayan fafatawa da sojoji suka yi da 'yan ta'adda a cikin daji, sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su.
Rahotanni da aka samu daga jami'an tsaro sun nuna cewa sojojin sun farmaki 'yan ta'addan ne cikin dare baya samun bayanan sirri game da su.
Asali: Legit.ng

