DSS Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta ba Wani da Aka Yi Zargin Dan Boko Haram Ne Diyya

DSS Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta ba Wani da Aka Yi Zargin Dan Boko Haram Ne Diyya

  • Hukumar DSS ta yi bincike tare da tabbatar da wanke wani da take zargin yana da alaka da Boko Haram
  • Daraktan DSS, Oluwatosin Ajayi, ya ba da umarnin sakin Nura Idris tare da alkawarin taimaka masa ya farfado da kasuwancinsa
  • DSS ta ce tana nazartar tsofaffin shari’o’i domin tabbatar da adalci, inda ta saki mutane da dama tare da ba su diyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Daraktan Hukumar Tsaro ta farin kaya, DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya bayar da umarnin sake wani da ake zargi da alaka da Boko Haram.

Hukumar ta saki Nura Idris bayan wani cikakken bincike ya wanke shi daga zargin alaka da kungiyar Boko Haram.

DSS ta sake wani da aka yi zargin na da alaka da Boko Haram
Nura Idris da aka yi zargin na da alaka da Boko Haram da shugaban hukumar DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi. Hoto: DSS Unofficial.
Source: Facebook

Idris, wanda manomi ne kuma mai kiwon dabbobi daga karamar hukumar Soba ta Kaduna, ya shiga hannu ne a Suleja cikin shekarar 2024 bisa zargin alaka da ‘yan ta’adda, cewar ThisDay.

Kara karanta wannan

Nnaji: Tsohon ministan Tinubu ya garzaya kotun dukaka kara bayan bada umarnin kama shi

Boko Haram: Binciken da aka yi kan Nura

Bayan an mika shi hannun DSS, kwamitin bincike na cikin gida ya sake nazarin shari’arsa tare da gano cewa babu wata hujja da ke tabbatar da zarge-zargen.

Sakamakon haka, Darakta Janar na DSS ya ba da umarnin a sake shi nan take tare da amincewa a ba shi tallafin Naira miliyan uku domin biyan bukatunsa na gaggawa.

Majiyar tsaro ta bayyana cewa hukumar DSS za ta kuma taimaka wa Idris wajen sake kafa kasuwancinsa domin ya samu damar komawa rayuwarsa ta yau da kullum.

DSS ta biya diyya ga wani da ta yi zargi da ta'addanci
Shugaban Hukumar DSS a Najeriya, Oluwatosin Adeola Ajayi. Hoto: Emma Courage.
Source: Facebook

Abin da Nura ya ce ga DSS

Da yake karbar tallafin, Idris ya gode wa shugaban DSS, yana mai cewa an kula da shi yadda ya kamata yayin da yake tsare, kamar yadda Daily Post ta ce.

Mahaifinsa, Yusuf Idris, shi ma ya nuna godiya bisa tausayi da karamcin da aka nuna wa dansa, tare da alkawarin amfani da kudin yadda ya dace.

Kara karanta wannan

'Isra'ila ta hallaka dubban yara kanana da gangan a Falasdinu'

Majiyar ta kara da cewa DSS kan samar da taimakon lafiyar kwakwalwa da na jinya ga wadanda aka wanke daga zargi kafin a taimaka musu wajen sake tsayawa da kafafunsu.

Wannan mataki wani bangare ne na nazarin tsofaffin shari’o’i da DSS ta fara domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da tsare marasa laifi ba tare da hujja.

Hukumar ta ce irin wadannan matakai suna nuna yadda take kokarin hada tsaron kasa da kare mutunci da hakkokin ‘yan Najeriya a karkashin jagorancin yanzu.

Wannan mataki wani bangare ne na nazarin tsofaffin shari’o’i da DSS ta fara domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da tsare marasa laifi ba tare da hujja.

Kuskuren zargin ta'addanci: DSS ta saki mutum 3

A wani labarin, an ji cewa Hukumar DSS ta bada umarnin sakin wasu mutane uku da aka tsare saboda zarginsu da ta'addanci.

Shugaban hukumar, Oluwatosin Ajayi shi ya bada umarnin sakin mutanen bayan binciken hukumar ya tabbatar da ba su da laifi.

Mutanen da aka saki sun gode wa hukumar, suna cewa an kula da su cikin mutunci, kuma babu wani cin mutunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.