Sassan Kano da Jihohin Arewa 5 da za a Dauke Wuta domin Gyara
- TCN ta sanar da cewa za a katse wutar lantarki na ɗan lokaci a sassa jihohi 5 a Najeriya da suka hada da Kano da Gazaoua a kasar Nijar
- Hakan zai biyo bayan aikin gyara da inganta tashar wutar lantarki ta 330kV da ke yankin Kumbotso, wanda za a gudanar a ranar Lahadi
- Aikin zai shafi kamfanonin rarraba wutar lantarki da suka hada da KEDCO, JEDC da YEDC da ke aiki a sassan Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da katsewar wutar lantarki na ɗan lokaci a wasu sassan jihohin Arewacin Najeriya.
Kamfanin TCN ya sanar da haka ne sakamakon aikin gyara da aka tsara gudanarwa a tashar wutar lantarki mai ƙarfin kilovolt 330 ta Kumbotso.

Source: Facebook
Tribune ta rahoto cewa TCN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ndidi Mbah, ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce an shirya gudanar da aikin gyaran a ranar Lahadi, 28 ga Yunin 2026.
Jihohin da za a dauke wuta
Rahhotanni sun nuna cewa wuraren da za su fuskanci matsalar wuta sun hada da sassan Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da Yobe, da kuma Gazaoua a Jamhuriyar Nijar.
A cewar kamfanin, katsewar wutar da aka tsara za ta bai wa kamfanin da ke aikin kwangilar damar ci gaba da inganta ayyuakansu
Za su yi aiki ne domin inganta wayoyin layin wuta na 330kV Bus II da kuma maye gurbin wayoyin 350mm² da ake amfani da su a yanzu da sababbi masu ƙarfin 800mm² domin ƙarfafa tsarin raba wutar lantarki na ƙasa.
Yankunan da abin zai shafa
Aikin gyaran zai shafi samar da wutar lantarki ga abokan huldar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), wasu sassan kamfanin Jos na JEDC da na Yola YEDC.
Channels TV ta rahoto cewa TCN ya ce:
“An tsara aikin gyaran ne domin bai wa kamfanin da ke aikin kwangila damar ci gaba da aikin inganta wayoyin 330kV Bus II da kuma maye gurbin wayoyin 350mm² da ake amfani da su da sabbin wayoyi 800mm² domin ƙarfafa tsarin sufurin wutar lantarki da inganta amincin samar da wuta."
“Sakamakon haka, Kamfanonin KEDCO, JEDC da YEDC ba za su iya samun wutar lantarki domin rarrabawa ga abokan cinikinsu a jihohin Kano, Katsina da Jigawa ba, da kuma Azare a Jihar Bauchi, Nguru a Jihar Yobe, da kuma Gazaoua a Jamhuriyar Nijar,”

Source: Facebook
TCN ta bayyana cewa aikin inganta tsarin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa kayayyakin aikin sufurin wutar lantarki da kuma inganta amincin da daidaiton samar da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.
Dangote zai shiga harkar lantarki
A wani labarin, mun kawo muku cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da cewa zai kutsa harkokin wutar lantarki a Najeriya.
A shirin da ya yi, Aliko Dangote ya sanar da cewa zai samar da wutar da ba za ta gaza megawatt 20,000 ba idan ya fara aiki a bangaren.
Dan kasuwar ya kara da cewa ya dauki matakin ne domin kawo karshen matsalar wutar lantarki da ta addabi Najeriya tsawon shekaru.
Asali: Legit.ng


