Mutane Sun Kama Malamar Islamiyya da Karfi Sun Kona Ta, 'Yan Sanda Sun Magantu

Mutane Sun Kama Malamar Islamiyya da Karfi Sun Kona Ta, 'Yan Sanda Sun Magantu

  • Rahoto ya nuna cewa wasu mutane sun kashe wata mata da aka ce malamar Islamiyya ce tare da kona gawarta a Maraban Jos a jihar Kaduna
  • An bayyana cewa da farko ta shiga ofishin 'yan sanda amma tarin mutane suka mamaye shi, suka fitar da ita suka kashe ta kan zargi maras tushe
  • Biyo bayan lamarin, rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce ta kama wasu mutane inda ta ce za a hukunta wanda aka samu da laifi ba sani ba sabo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce wasu fusatattun mutane sun kashe wata malamar Islamiyya tare da kona gawarta a ranar Lahadi, 21 ga Yunin 2026.

Rahotanni da aka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa an kashe matar ne bisa zargin satar yara a yankin Maraban Jos da ke jihar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An rushe katafaren gidan kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka cafke a Edo

Malamar Islamiyyar da aka kashe a Kaduna
Wajen da aka kona malamar Islamiyya a hagu, kwamishinan 'yan sandan Kaduna a dama. Hoto: Mansur Hassan|Aliyu Haidar
Source: Facebook

An kashe malamar Islamiyya

NTA a ta wallafa a Facebook cewa kakakin rundunar, Mansur Hassan, ya bayyana a wata sanarwa cewa da misalin karfe 10:00 na safe suka samu labarin lamarin.

Ya ce jami'in kula da ofishin 'yan sanda na Maraban Jos ya samu kiran gaggawa cewa wasu mutane sun kai wa wata mata hari bisa zargin satar yara ba tare da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba.

Mansur Hassan ya ce jami'in ya jagoranci jami'ansa zuwa wurin, inda suka ceto matar tare da kai ta ofishin 'yan sanda domin ba ta kariya da kuma gudanar da bincike.

"Duk da haka, daga baya wani babban taro na mutane da yawansu ya kai daruruwa ya mamaye ofishin 'yan sanda, suka yi nasarar rinjayar jami'an da ke bakin aiki, suka fitar da matar daga tsare, suka kashe ta sannan suka kona gawarta,"

In ji sanarwar.

Game da unguwar da matar ta ke, 'yan sanda sun ce:

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bindige dan ta'adda mai garkuwa da mutane

"Marigayiyar 'yar asalin Maraban Jos ce. Rundunar tana kallon wannan aiki a matsayin dabbanci, laifi, da kuma katsalandan kai tsaye ga doka da oda.
"Babu wani mutum ko rukuni da ke da ikon daukar doka a hannunsa."
Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

'Yan sanda sun kama mutane

The Cable ta wallafa cewa kakakin 'yan sandan ya ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da farautar sauran wadanda suka tsere.

"An fara cikakken bincike, kuma duk wadanda aka samu da hannu za su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada."

Ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Muhammad, ya gargadi cewa rundunar ba za ta lamunci daukar doka a hannu ba, tayar da tarzoma, ko kai hare-hare kan ofisoshi da jami'an 'yan sanda ba.

Ya kara da cewa:

"Ana kira ga jama'a da su rika sanar da 'yan sanda duk wani mutum ko abu da suke zargi da shi, tare da barin hukumomi su bi hanyoyin da doka ta tanada.
"Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da adalci bisa tanadin doka."

Kara karanta wannan

An fallasa shirin shawo kan talaka da shinkafa da taliya a zaben gwamnan Ekiti

Matar Sheikh Pakistan ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa an sanar da rasuwar matar tsohon shugaban NAHCON kuma shugaban Izala na jihar Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan.

Matar mai suna Hajiya Zainab ta rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya da ta yi, lamarin da ya kai ga kwantar da ita a wani asibiti.

Tuni aka gudanar da sallar jana'izar marigayiyar a ranar Asabar da ta wuce a jihar Kano, inda manyan malamai da sauran jama'a suka hallara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng