Trump Ya Jawo Sabon Fada da Iran Ta kai Hare Haren kan Amurka
- Iran ta kai hare-haren ramakon gayya kan wuraren da ke da alaƙa da sojojin Amurka bayan hare-haren saman da Amurka ta kai Tehran
- Iran ta kuma ƙaddamar da hare-hare da jiragen yaki zuwa kasar Bahrain bayan ta farmaki wani jirgin dakon da ya so wucewa ta Hormuz
- Yayin da rikici ke son dawowa Gabas ta Tsakiya, gwamnatin Bahrain ta sanar da cewa harin babbar barazana ne ga tsaron ƙasar da mazauna cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Iran ta ce ta kai hare-hare kan wuraren da ke da alaƙa da dakarun Amurka domin mayar da martani ga hare-haren saman da Amurka ta kai a gabar tekunta.
Iran ta ce hare-haren Amurka sun saɓa wa kundin tsarin majalisar dinkin duniya da kuma yarjejeniyar dakatar da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

Source: Getty Images
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar ya ce bayanin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fitar.
Iran ta kai hari a kasar Bahrain
Iran ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da suka nufi Bahrain, yayin da wani jirgin ruwa a mashigin Hormuz ya fuskanci hari a ranar Asabar.
Rahoton AP ya nuna cewa ana ganin mai yiwuwa ne harin Iran ya kasance martani ne ga hare-haren saman da Amurka ta kai mata cikin dare.
Hare-haren da aka kai a yankin Tekun Farisa sun nuna haɗarin rikicin Iran na sake tsananta duk da cewa Iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar wucin-gadi domin ƙoƙarin cimma cikakkiyar yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen rikicin.
Amurka ta kai hare-haren saman ne bayan wani hari da Iran ta kai da jirgi maras matuƙi kan wani jirgin ruwa da ke ƙoƙarin ficewa daga mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Martanin kasar Bahrain ga Iran
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Bahrain ta ce jirage marasa matuƙa da dama na Iran sun kai hari kan ƙasar.
A sanarwar da Bahrain ta fitar ta bayyana harin a matsayin:
“Babbar barazana ga tsaron 'yan ƙasa da mazauna ƙasar.”
Tun da farko, rundunar Iran ta fitar da wata sanarwa tana cewa ta kai hari kan wurare da dama “na rundunar ta'addancin Amurka a yankin.”
A lokaci guda, cibiyar kula da harkokin cinikayyar jiragen ruwa ta rundunar sojin Birtaniya, ta ce an kai hari kan wani jirgin dakon mai a mashigar Hormuz a ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026.
Amurka ta rage takunkumin Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Donald Trump ta rage takunkumin da ta kakabawa 'yan kwallon kafar kasar Iran.
Dage takunkumin zai saukakawa 'yan kwallon Iran zirga-zirga yayin da suke buga gasar cin kofin duniya ta 2026 a kasar Amurka.
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta dauki matakin ne bayan cimma yarjejeniya da kasar Iran bayan tattaunawa da suka yi a makon da ya wuce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

