Hankulan Mutane Sun Tashi kan Yadda Aka Tsinci Gawar Budurwa a Ɗakin Saurayinta

Hankulan Mutane Sun Tashi kan Yadda Aka Tsinci Gawar Budurwa a Ɗakin Saurayinta

  • Jami'an tsaro sun kama wani mutum mai suna Joe bayan an tsinci gawar budurwarsa a gidansa da ke Warri, jihar Delta
  • Lamarin ya faru ne a unguwar Edjeba bayan matar ta kai masa ziyara, inda azauna suka ce sun ga matar cikin ƙoshin lafiya kwana ɗaya kafin rasuwarta
  • Dakarun 'yan sanda sun ce sun fara bincike, yayin da aka kai gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa domin bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta cafke wani mutum mai suna Joe bayan an tsinci gawar budurwarsa a cikin gidan da yake zaune a unguwar Edjeba da ke Warri.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga Yunin 2026, bayan matar ta kai masa ziyara a gidansa da ke titin Ajidi.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

Delta.
Taswirar jihar Delta da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda matar ta ziyarci saurayinta

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu majiyoyi daga yankin da lamarin ya auku sun bayyana cewa mamaciyar da wanda ake zargin sun shafe kwanaki suna tare a gidan kafin rasuwarta.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an ga matar tana yawo cikin unguwar cikin ƙoshin lafiya kwana ɗaya kafin mutuwarta.

Mutumin ya ce:

"Mun ga matar jiya tana yawo a unguwa cikin ƙoshin lafiya. Babu wanda ya yi tunanin cewa zuwa safiyar yau za a samu labarin cewa ta mutu. Lamarin ya tayar da hankali jama'a matuƙa."

Dalilin da ya sa aka kira jami'an tsaro

Majiyar ta ƙara da cewa da sanyin safiyar ranar Laraba da ta gabata, mazauna yankin sun ji ƙarar ihu daga gidan da Joe ke zaune, lamarin da ya tada masu da hankali.

A cewar majiyar, hakan ya sa mai gidan ya sanar da jami'an tsaro, inda 'yan sanda suka isa wurin domin gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

Bayan sun shiga ɗakin, jami'an tsaro sun tarar da gawar matar a cikin ɗakin wanda ake zargin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Yan sanda.
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya suna aikin sintiri don tabbatar da tsaro Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun fara bincike

Rahotanni sun ce an kama Joe tare da tsare shi domin ci gaba da bincike, yayin da aka kai gawar mamaciyar zuwa ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike da kuma yiwuwar gwajin gano musabbabin mutuwa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi ƙarin bayani ba, yana mai cewa bincike yana ci gaba.

Ɗan kasuwa ya mutu a ɗakin yar TikTok

A wani rahoton, kun ji cewa wani matashin ɗan kasuwa, Isma’il Makaye, ya mutu a gidan budurwarsa yar TikTok, Fati Cele da ke Danbare a jihar Kano.

Wani abokin marigayin mai suna Hassan Mohammed, wanda yana cikin wadanda suka je wurin tare da jami’an ‘yan sanda, ya ce lokacin da suka isa gidan sun tarar da gawar matashin.

Hassan ya kara da cewa Makaye da Fati Cele sun shafe sama da shekaru biyu suna soyayya kafin su rabu na wani lokaci bayanNmamacin ya yi aure, daga bisani kuma suka sake sulhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262