Filato: Gwamnati Ta Fito da Bayanai kan Zargin DSS da Yi Mata Zagon Kasa

Filato: Gwamnati Ta Fito da Bayanai kan Zargin DSS da Yi Mata Zagon Kasa

  • Gwamnatin jihar Filato ta ce babu wani lokaci da hukumar DSS ta kawo cikas ko ta hana mata daukar matakan kare al’ummarta
  • Wannan bayani ya biyo bayan wani labari da ke cewa jami'an DSS sun kwace wasu makamai da gwamnati ta sayo wa jami'anta
  • Gwamnati ta ce an shirya wannan rahoto ne don jefa fitina tsakanin bangarorin gwamnati da hukumomin tsaro da ke kare jama'a
  • Sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau, ya fitar, ta ce DSS na daga cikin manyan hukumomin da ke taimaka masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar PlateauGwamnatin Filato ta karyata rahotannin da ke cewa hukumar DSS ta hana ko ta yi katsalandan a kokarinta na mayar da martani kan hare-haren 'yan bindiga da suka addabe su.

A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau, ya fitar a ranar Talata, gwamnatin ta bayyana rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da cewa karya ne.

Plateau
Gwamnatin Filato ta karyata cewa DSS na jawo mata matsalar aiki Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Facebook

A sakon da aka wallafa a shafin Facebook na gwamnatin Filato, an bayyana rahoton a matsayin yaudara, da aka kirkira domin jefa rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da DSS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Filato ta yabi hukumar DSS

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin Filato ta bayyana hukumar DSS a matsayin abokiyar a yakin da take yi da matsalar rashin tsaro.

Haka kuma ta jaddada cewa DSS ta taimaka sosai wajen ganin an rage yawan hare-hare da ayyukan ta’addanci a jihar.

Gwamnatin ta bukaci al’umma da su yi watsi da rahoton cewa hukumar tsaron na yi mata katsalandan, tana mai cewa babu gaskiya ko kadan a cikinsa.

Gwamnatin Filato ta soki rahoton shafukan zumunta

Gwamnatin Filato ta soki labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta, tana mai cewa ba a taba samun wani lokaci da DSS ta hana ta tabbatar da tsaro a jihar ba.

Caleb
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce:

“Rahotannin da aka gani a Facebook da sauran shafukan sada zumunta suna dauke da labarin karya wanda ke cewa DSS ta kwace makaman da aka tanada domin hukumar tsaron al’umma ta jihar – Operation Rainbow.”

Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin nan gaba daya, tana mai cewa “karya ne karara, kuma ba su da tushe balle makama.”

Gwamnatin Filato ta koka da rashin tsaro

A baya, mun kawo labarin cewa gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa tun lokacin da aka fara mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya a shekarar 1999, ake fama da rashin tsaro a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da manyan ‘yan asalin jihar da aka gudanar don nazari da fitar da mafita kan yawaitar kisan gillar da ake fama da shi a sassan Filato.

Gwamnan ya ce rahotannin sirri da gwamnati ke da su sun tabbatar da cewa wuraren da ya kamata a kasance na amfanin al’umma, sun zama maboyar miyagun mutane a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.