Kano: Abba Ya Biya N21bn cikin N48.6bn da Ganduje Ya Gaza Biyan 'Yan Fansho
- Hukumar fansho ta Kano ta ce ta riga ta biya fiye da Naira biliyan 21 daga cikin bashin da tsofaffin ma’aikata ke bin gwamnati
- Shugaban hukumar, Alhaji Habu Fagge da ya bayyana haka, ya ce gwamnatinsu ta gaji bashin Naira biliyan 48.6 daga Abdullahi Ganduje
- Hukumar ta zargi gwamnatin da ta gabata da cire kudin fansho ba bisa ka’ida ba, har ma da rance daga asusun fansho
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar kula da kudin fansho ta Kano ta bayyana cewa ta riga ta biya bashin da ya haura N21bn daga cikin jimillar N8.6bn da tsofaffin ma'aikata ke bin gwamnatin jihar.
Shugaban hukumar kula da fansho na jihar, Alhaji Habu Fagge, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Alhaji Habu Fagge ya ce bashin da ake bi ya kasance gado ne daga gwamnatocin baya da suka yi mulki a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta biya kudin ‘yan fansho
Jaridar Vanguard ta kuma bayyana cewa Alhaji Habu Fagge ya ce sun karbi shugabancin hukumar cikin yanayi mai cike da kalubale.
Ya ce:
“’Yan fansho sun sha wahala ta hanyar cire musu kudi ba bisa ka’ida ba a karkashin gwamnatin da ta gabata.
Wasu lokutan ana cire rabin abin da suke karba duk wata, ba tare da wani karin bayani ba."
A wani lokaci, ana cirewa wanda ke karbar N6,000 har N3,000 ba tare da an fadi dalili ba. Babu wani tsari ko ka’idar da aka bi wajen wadannan cire-ciren.”
Kano: Yadda gwamnati ta ranci kudin ‘yan fansho
A cewar Alhaji Fagge, gwamnatin da ta gabata, a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta ranci kudi daga asusun fansho.
Ya bayyana cewa kokarin dawo da wadannan kudade ya fara ne lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da a rika cire kudin fansho kai tsaye daga tushen kudaden shiga na gwamnati.
Haka nan, gwamnan ya dawo da tsarin biyan fansho akai-akai, wanda hakan ya bai wa hukumar damar biyan 100% na kudaden fansho na kowane wata.

Asali: Facebook
Shugaban hukumar ya ce:
“Mun gaji bashin fansho na N48.6bn, sannan muna da wajibcin biyan N75bn da aka dora wa kananan hukumomi da wasu hukumomin gwamnati (MDAs)."
Duk da haka, mun riga mun biya N16bn, sannan muna shirin fitar da karin N5bn domin ci gaba da biyan hakkokin.”
Ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf bisa nuna tausayi da damuwa da halin da ‘yan fansho ke ciki, yana mai cewa:
“Ko da yake wannan bashi ne da aka gada, gwamnan ya dauki nauyin biyan sa, domin kulawa da jin dadin ‘yan fansho kawai.”
Gwamnatin Kano ta waiwayi 'yan fansho
A baya, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da mataki na uku na biyan hakkokin 'yan fansho, domin rage radadin wahala ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati.
Ana sa ran matakin zai shafi biyan kudade da suka kai kimanin N5bn, a matsayin wani bangare na shirin gwamnatin Kano na biyewa da alƙawuran da aka dauka ga tsoffin ma’aikata.
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada cewa ta damu da jin dadin 'yan fansho, kuma tana daukar biyan hakkokinsu a matsayin muhimmin ginshiki na kyautata rayuwar tsofaffin ma'aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng