Harin 'Yan Bindiga: Yadda Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya da baya
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Kalanjeni da ke ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto
- Harin da ƴan bindiga suka kai a ranar Laraba, ya kusa ritsawa da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Isa Kalanjeni
- Bayan sun kasa cimma Isa Kalanjeni, ƴan bindigan sun sauke fushinsu a kan mutanen ƙauyen, suka yi ɓarna mai tarin yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Harin ƴan bindiga ya jawo tashin hankali ya mamaye mazauna ƙauyen Kalanjeni da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Miyagun ƴan bindigan waɗanda suka mamaye ƙauyen da tsakar rana, sun kusa kama shugaban ƙaramar hukumar, Isah Kalanjeni.

Asali: Original
Shugaban ƙaramar hukuma ya sha da ƙyar
Jaridar Vanguard ta ce shugaban ƙaramar hukumar, wanda kuma ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya har sau biyu, ya bar gidansa da ƴan mintuna kaɗan kafin ƴan bindigan su iso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya kasance kamar fim, yayin da mazauna ƙauyen suka ranta ana kare don tsira daga harbe-harben bindiga.
Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne a kan babura masu yawa.
“Abin ya zama kamar fim ne. Sun shigo da fiye da babura 30, suna harbe-harbe a sama."
"Mun godewa Allah da shugaban ƙaramar hukumar ya tafi tun da wuri, da yanzu sun kama shi."
- Wani mazaunin ƙauyen
Wata majiya kusa da shugaban ƙaramar hukumar ta bayyana cewa tafiyar da ya yi ba a shirya ta ba.
Ƙauyen Kalanjeni da ke da nisan kimanin kilomita 40 daga babban birnin Sokoto, yana fama da matsalar rashin tsaro.
Tangaza na daga cikin ƙananan hukumomi 13 a jihar Sokoto da ke fama da barazanar ƴan bindiga, ciki har da garkuwa da mutane, satar shanu da ƙone ƙauyuka.
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Sokoto
Shaidu sun ce bayan da ƴan bindigan suka kasa samun wanda suka zo nema, sai suka juye fushinsu kan mazauna ƙauyen, inda suka sace dabbobi da dama tare da lalata dukiyoyin jama’a.
Wani makiyayi a ƙauyen mai suna Malam Abdullahi ya bayyana cewa an kwashe musu shanu da awakai.
“Sun kwashe shanunmu da awakinmu. Babu abin da ya rage mana."
- Malam Abdullahi
Abin da ƴan sanda suka ce kan harin

Asali: Twitter
Da yake mayar da martani game da lamarin, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, Ahmad Rufa’i, ya tabbatarwa Legit Hausa da aukuwar harin, amma ya ƙi bayar da cikakken bayani.
"Jami’anmu tare da sojoji sun isa yankin, bayan musayar wuta mai tsanani, ƴan bindigan sun janye kuma suka bar yawancin dabbobin da suka sace. Ana ci gaba da gudanar da bincike."
- DSP Ahmad Rufai
Ƴan bindiga sun kai hari a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Ƴan bindigan waɗanda suka ɓuɗewa mutane wuta a wata tashar mota, sun hallaka mutum shida har lahira.
Jami'an ƴan sanda waɗanda suka tabbatar da aukuwar harin, sun bayyana cewa an cafke mutum ɗaya wanda yake ba ƴan bindiga bayanai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng