Nuhu Ribadu Ya Jajanta kan Kashe Kashe a Benue, Ya Fadi Shirin Shugaba Tinubu
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya je jihar Benue kan hare-haren ƴan bindiga
- Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwammatin tarayya ta tashi tsaye domin magance matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar
- Ribadu ya ce Shugaba Bola Tinubu yana tare da mutanen jihar a wannan mawuyacin lokacin da suka tsinci kansu a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya kan rashin tsaro a jihar Benue.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar Benue.

Asali: Facebook
Ribadu ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar Benue, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron ne a ranar Talata bayan kisan fiye da mutane 72 da ya faru a ƙananan hukumomin Ukum da Logo a ranar Good Friday.
Saƙon Tinubu da Nuhu Ribadu ya kawo
Nuhu Ribadu ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayyana a fili cewa yana tare da jihar Benue kan matsalar tsaron da take fuskanta, inda ya ƙara da cewa duk faɗin ƙasar na fama da irin wannan matsala.
Yayin da yake bayyana kisan da aka yi a matsayin babban masifa ga ƙasa baki ɗaya, Ribadu ya ce sharri ne ya ziyarci jihar.
"Na zo nan domin na yi ta’aziyya da ku da mutanen jihar Benue bisa wannan babban rashi, da kuma tabbatar muku cewa ƙasar nan tana tare da ku."
“Shugaban ƙasa yana tare da ku. Wannan wani lokaci ne mai wuya gare mu baki ɗaya. Lokaci ne na baƙin ciki, kuma irin waɗannan lokuta ne ke nuna waɗanda ke da gaske suna tare da ku."
"Abin da ya faru babban bala’i ne, sharri ne. Amma idan sharri ya zo, to nagartattun mutane su haɗa kai don fuskantar sa."
"Benue jiha ce mai matuƙar muhimmanci a Najeriya. A matsayinku na rumbun abinci na ƙasa, kuna kan gaba wajen samar da abinci, kuma muna alfahari da ku."
"Zamu fuskanci wannan matsala tare. Ka da ku ji cewa ku kaɗai ne, wannan ƙalubale ya shafi kowa."
- Nuhu Ribadu
Gwamnatin Bola Tinubu na bakin ƙoƙarinta

Asali: Facebook
“Dakarunmu da hukumomin tsaro suna bakin ƙoƙarinsu, amma irin waɗannan abubuwa na faruwa saboda ba zai yiwu a tura jami’an tsaro zuwa kowanne ƙauye ba."
“Kowace ƙasa tana fuskantar irin na ta matsalolin. Rashin tsaro babbar matsala ce da ke buƙatar juriya da haɗin kai."
“Yin barna abu ne mai sauƙi, amma warware matsalolin da ke haddasa barnar shi ne babban ƙalubale, duk da haka muna yin bakin ƙoƙarinmu."
- Nuhu Ribadu
Gwamnan Benue ya faɗi masu kai hari a jihar
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia,.ya bayyana cewa masu kai hari a jihar ba ƴan Najeriya ba ne.
Gwamna Alia ya bayyana cewa maharan ba daga Nakeriya suke ba, domin suna magane ne da wani irin yare na daban.
Ya ƙara da cewa maharan waɗanda suke ɗauke da bindigu ƙirar AK-47 da AK-49 ba su yi kama da ƴan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng