Ribadu, Gwamnan Binuwai Sun Saba a kan Girman Matsalar Tsaron Najeriya

Ribadu, Gwamnan Binuwai Sun Saba a kan Girman Matsalar Tsaron Najeriya

  • Gwamna Binuwai, Hyacinth Alia ya koka kan yawan hare-haren 'yan bindiga a jiharsa, yana mai cewa 'yan bindiga na cin karensu babu babbaka
  • Ya kara da cewa 'yan bindiga sun samu mafaka a wasu wurar, inda daga nan ne suka kai hari cikin jama'a, tare da salwantar da daruruwan rayuka
  • Amma a jawabinsa, Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce babu wurin da ke karkashin ikon 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar BenueGwamnan Binuwa, Hyacinth Alia, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, sun bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da halin tsaro a jihar.

Gwamna Alia ya bayyana jihar a matsayin wadda ke fama da matsanancin farmaki daga ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da kungiyoyin makamai.

Binuwai
Nuhu Ribadu ya ce babu wurin da ke karkashin ikon yan ta'adda Hoto: Fr. Hyacinth lormen Alia/Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya ce wadannan hare-hare na ci gaba da durkusar da tattalin arzikin al’umma da kuma raba dubban mazauna muhallinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma ya koka da yadda 'yan bindiga suka mamaye wasu wurare, tare da kai hare-haren da ake shirya su, kuma ana maimaita su a kai a kai.

Abin da Nuhu Ribadu ya ce kan rashin tsaro

Trust Radio ta wallafa Nuhu Ribadu ya amince da cewa akwai barazanar tsaro a yankin, amma ya jaddada cewa babu wani bangare na Najeriya da ke karkashin ikon wasu kungiyoyin 'yan ta'adda.

Wannan furuci na Ribadu na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke kara muni a yankin Sankera na Jihar Binuwai, wanda ya kunshi kananan hukumomin Ukum, Katsina-Ala da Logo.

Rahotanni sun ce hare-haren da aka shirya cikin tsari sun jawo asarar rayuka da dukiyoyi a wadannan yankuna, yayin da jama'a ke zaman dar-dar.

Rashin tsaro na kara kamari a Binuwai

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Afia da ke karamar hukumar Ukum a ranar Talata.

Binuwai
Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia Hoto: Fr. Hyacinth lormen Alia
Asali: Facebook

Wannan ya kai adadin wadanda aka kashe a cikin kwana biyar da suka gabata zuwa 83, sakamakon jerin hare-haren ‘yan bindiga.

Daga ranar Litinin, 21 ga Afrilu, adadin wadanda aka kashe ya kai 72, inda aka rika gano karin gawarwaki a yankunan da abin ya shafa tun daga ranar Alhamis, 17 ga Afrilu.

An shaidawa Ribadu girman matsalar tsaron Binuwai

Sarkin gargajiya na Ukum, Cif Orkaa Kaave, ya bayyana sabon harin ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, a ranar Talata.

Cif Kaave ya ce:

“Yau (Talata), a garin Afia—inda Sanata Emmanuel Udende ke zaune—kisan na ci gaba da faruwa. Zuwa yanzu mun gano gawarwaki 11, amma har yanzu ana ci gaba da bincike a dazuka. Wannan sabon hari ne, kuma yana faruwa yanzu haka.”

Ribadu ya amince akwai rashin tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta gaji rashin tsaro daga gwamnatin baya.

Sai dai ya ce, ko da yake matsalar ta dabaibaye sassan kasar, gwamnati na ci gaba da aiki tukuru ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya, kuma yanzu haka an fara ganin sauyi.

Ya fadi haka ne yayin taron tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati na Binuwai da ke Makurdi, tare da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar don kawo karshen matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.