Dokar Ta Baci: Gwamna Alia Ya Bukaci Taimakon Tinubu kan Tsaro

Dokar Ta Baci: Gwamna Alia Ya Bukaci Taimakon Tinubu kan Tsaro

  • Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa abin da al’ummarsa ke buƙata yanzu shi ne cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya, ba dokar ta-baci ba
  • Ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar ba ta fi ƙarfinsa ba, amma yana neman taimako sosai domin ya kori makiyaya masu ɗauke da makamai a fadin jihar
  • Gwamna Hyacinth Alia ya jaddada cewa gwamnatinsa ta rage yawan kananan hukumomin da ake kai hare-hare daga 17 zuwa shida bayan hawansa kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fi mayar da hankali kan tallafa wa jihar ta fuskar tsaro.

Ya bayyana cewa goyon baya suke bukata a yanzu maimakon shirin kakabawa jihar dokar ta-baci kan matsalar tsaro da suke fuskanta.

Gwamnan Benue
Gwamnan Alia ya ce babu bukatar dokar ta baci a Benue. Hoto: Benue State Government
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV a wani shirin da tashar ta yi a yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, matsalar hare-haren makiyaya da suka addabi al’umma a wasu yankuna ba ta kai ga bukatar dokar ta-baci ba.

Gwamnan ya kara da cewa har yanzu gwamnatinsa na iya shawo kan lamarin idan aka samu ƙarin tallafi daga gwamnatin tarayya.

'Benue na bukatar taimako,' Gwamna Alia

Gwamna Alia ya bayyana cewa tun bayan da ya karɓi mulki, an sami gagarumar nasara wajen rage yawan hare-haren da ake kai wa al’umma a sassan jihar.

Ya ce kafin ya zamo gwamna, ana kai hare-hare a kananan hukumomi 17, amma yanzu hakan ya ragu zuwa guda shida.

A karkashin haka ya ce hakan na nuna cewa akwai ƙarfin ikon shawo kan matsalar idan aka samu cikakken hadin kai.

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan ya ce:

“Ba dokar ta-baci muke buƙata ba. Muna buƙatar taimakon gaggawa ne kawai.
"Gwamnatin tarayya ta turo manyan motocin yaki guda biyu, kuma tun daga nan abubuwa suka fara sauyawa.”

'Yan kasar waje na kai hari Benue,' Alia

Gwamnan ya bayyana cewa yawancin makiyayan da ke kai hare-haren ba ’yan Najeriya ba ne, domin ba su iya yarukan da ake amfani da su a jihar.

Alia ya ce:

“Wadanda suka mamaye ƙasarmu ba ’yan Najeriya ba ne. Muna buƙatar taimako domin fitar da su daga ƙasashenmu, mu dawo da manoma cikin gonakinsu na gado.”

Alia ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ƙara zurfafa hadin gwiwa da gwamnatin jiharsa domin dawo da zaman lafiya da walwala ga al’ummar da rikice-rikicen suka rutsa da su.

Gwamnan Benue
Gwamnan Benue ya bukaci karin agaji daga gwamnatin tarayya kan tsaro. Hoto: Benue State Government
Asali: Twitter

'Yan Mahmuda sun zafafa hare hare a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar 'yan ta'adda ta Mahmuda ta fara kai hare hare masu zafi a yankunan Arewa ta Tsakiya da ta fara karfi.

An ruwaito cewa 'yan kungiyar sun kai wasu hare hare cikin dare tare da hallaka mutane da dama.

Domin shawo kan lamarin, gwamnan jihar Kwara ya kai ziyarar gani da ido wata karamar hukumar da 'yan ta'addan suka kai hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng