Ardo Risku: Gwamna Ya Shirya Daukar Mataki kan Hallaka Shugaban Miyetti Allah
- Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da kisan shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku da dan uwansa
- Alia ya ce kisan ya faru ne a lokacin da zaman lafiya ke kara dawowa a sassan Benue, yana mai cewa hakan barazana ce ga kokarin sulhu
- Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, su kamo masu hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Gwamnan Benue, Fasto Hyacinth Alia, ya bayyana matukar alhini da kaduwarsa bayan kisan shugaban Miyetti Allah.
Gwamnan ya sha alwashin daukar mataki game da kisan gilla da aka yi wa Alhaji Ardo Risku, da wani dan uwansa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Tersoo Kula, ya fitar a shafin Facebook a yau Asabar 27 ga watan Yunin 2026.
Benue: Gwamna ya ji takaicin kisan Ardo Risku
A cikin sanarwar, gwamnan ya ce wannan mummunan lamari ya faru ne a wani lokaci mai muhimmanci.
Ya bayyana cewa jihar Benue na ci gaba da samun dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kananan hukumomi da dama bayan dogon lokaci na matsalolin tsaro.
Gwamnan ya ce wannan kisa ba wai kawai abin takaici ba ne ga jihar, har ila yau wani yunkuri ne na lalata nasarorin zaman lafiya.
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan wani taron tsaro, abin da ya sa ya fi tayar da hankali da damuwa.
Ya ce:
"Abin takaici ne matuƙa cewa wannan mummunan lamari ya faru jim kaɗan bayan gudanar da wani taron tsaro."

Source: Twitter
Cikas da kisan Ardo zai kawo a Benue
Hyacinth Alia ya jaddada cewa kashe shugabannin al’umma ko masu fafutukar zaman lafiya na kawo cikas ga tattaunawar da ake yi tsakanin bangarori daban-daban.
Saboda haka ya umarci dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa su fara cikakken bincike cikin gaggawa domin gano hakikanin abin da ya faru.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ndume ya gano matsalar da Tinubu ke fuskanta a fadar shugaban kasa
Ya bukaci jami’an tsaro su nemo wadanda suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a gaban kuliya cikin sauri domin zama izina.
Gwamnan ya kuma bukaci a kara tsaurara matakan tsaro domin kare shugabannin al’umma da masu aikin samar da zaman lafiya a jihar.
Ya roki mambobin MACBAN da sauran jama’a su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka, tare da kauce wa duk wani tashin hankali.
Benue: Yan bindiga sun yi yunkurin kai hari
Mun ba ku labarin cewa dakarun Operation Whirl Stroke sun kama wani da ake zargi bayan dakile yunkurin ‘yan bindiga na kawo cikas ga zaben APC a Benue.
Sojojin sun kwato bindigar AK-47, harsasai da motar Sienna da ake zargin maharan sun shirya amfani da ita wajen tserewa bayan harin.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kuma cafke wasu da ake zargi da alaka da ‘yan ta’adda a jihohin Kwara da Benue a lokuta daban daban.
Asali: Legit.ng
