Da Gaske an Kama Fasto da Hannu a Sace Dalibai, Malamai? Yan Sanda Sun Magantu
- Rundunar ‘yan sandan Oyo ta yi karin haske kan zargin cewa an kama wani fasto da hannu a sace dalibai da malamai
- ‘Yan sanda sun ce babu wani fasto da suka kama ko wata hukumar tsaro da ta kama dangane da zargin safarar makamai
- Rundunar ta gargadi masu yada labaran karya tare da jaddada cewa tana ci gaba da kokarin ceto daliban da malaman da aka sace lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Rundunar ‘yan sandan Oyo ta yi martani kan rahotannin da ke yawo cewa an kama wani fasto da hannu a sace dalibai da malamai.
Rundunar ta ce babu gaskiya kan cafke faston a harin da aka kai a yankin Orire, tana mai bayyana labarin a matsayin karya da yaudara.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Olayinka Ayanlade, ya fitar wanda The Guardian ta samu.
Yan sanda sun magantu kan zargin cafke fasto
Rundunar ta ce babu wani fasto da ‘yan sanda ko wata hukumar tsaro da ke cikin aikin ceto wadanda aka sace suka kama, sabanin rahotannin da ke yawo.
Rahotannin sun zargi faston da samar da makamai da alburusai ga mutanen da ke da hannu wajen sace daliban da malamai, amma rundunar ta ce zargin ba gaskiya ba ne.
‘Yan sanda sun kara da cewa sakon da ya bazu a kafafen sada zumunta bai bayyana sunan faston ko adireshinsa ba, abin da ke nuna rashin gaskiyar hakan.
Sanarwar ta ce:
“Mun samu rahotanni na karya da yaudara da ke yawo a wasu kafafen yada labarai, wallafe-wallafen intanet wanda ke zargin cewa an kama wani fasto saboda samar da makamai da alburusai ga mutanen da ke da hannu wajen sace dalibai da malamai a Orire.
“Rundunar tana son bayyana karara cewa wannan ikirari karya ne gaba daya, mai cike da yaudara kuma ba shi da tushe.”

Source: Original
Gargadin da yan sanda suka yi
A cewar rundunar, an yada rahoton ne da gangan domin karkatar da hankalin jami’an tsaro daga kokarin ceto wadanda aka sace tare da rage amincewar jama’a.
Rundunar ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin tare da dogaro da sahihan bayanan da ake fitarwa ta hanyoyin sadarwa na hukuma kawai, cewar Punch.
Ta kuma gargadi mutane da dandamalin da ke yada labaran karya da su daina, tana mai cewa duk wanda aka samu yana yada bayanan da za su iya kawo cikas ga tsaro zai fuskanci hukunci.
Rundunar ‘yan sandan Oyo ta sake tabbatar da kudirinta na ganin an ceto dalibai da malaman da aka sace cikin koshin lafiya tare da tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Sace dalibai: Gwamna zai sadaukar da ransa
Mun ba ku labarin cewa dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace a Oyo na ci gaba da zama a tsare a cikin daji wata guda bayan da aka yi garkuwa da su.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa hukumomi na ci gaba da kokarin ganin an kubutar da su cikin aminci.
Seyi Makinde ya nuna cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa idan har hakan zai sanya yaran su kubuta daga hannun 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng


