Sola a Villa: Bayan Sako Tinubu a Gaba, Fadar Shugaban Kasa Ta Buga Misali da Amurka
- Fadar shugaban ƙasa ta kare amincewar majalisar zartarwa na yin amfani da N10bn wajen sanya na’urar samar da wuta ta hasken rana a Aso Rock
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, ya kwatanta shirin da irin abin da ya faru a Fadar White House a Amurka
- Wasu ‘yan Najeriya na ganin shirin yana da fa’ida, yayin da wasu ke kallon kudin da za a kashe bai dace da halin kuncin tattalin arziki da ake ciki ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yayin da ake ta ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya kan amincewar gwamnati na kashe Naira biliyan 10 wajen samar da sola a Aso Villa, fadar shugaban ƙasa ta yi martani.
Fadar shugaban kasa ta fito fili ta kare matakin bayan 'yan Najeriya sun matsa lamba ga Bola Tinubu kan lamarin.

Asali: Getty Images
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana a shafinsa na X cewa ko a fadar shugaban kasar Amurka ana amfani da sola.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Onanuga ya ce:
“Fadar shugaban ƙasar Amurka (White House) na amfani da sola”
Onanuga ya fadi haka ne domin nuna cewa amfani da wutar sola a muhimman wuraren gwamnati ba sabon abu ba ne.
Shirin samar da sola a fadar Aso Rock
Vanguard ta wallafa cewa wutar solar da za a samar a Aso Rock za taba da wuta mai ɗorewa ga gidan shugaban ƙasa, ofisoshin gudanarwa da kuma wasu muhimman gine-gine.
An bayyana cewa hakan zai ƙara inganta ingancin wutar lantarki da rage dogaro da na’urar janareto, tare da rage kuɗin da gwamnati ke kashewa kan lantarki a tsawon lokaci.
Onanuga ya haɗa da bidiyo na wani aikin samar da sola da aka aiwatar a Fadar White House, inda aka nuna dalilan da suka sa gwamnatin Amurka ta zaɓi amfani da sola a shekarun baya.
Ana amfani da sola a White House tun 1979
Rahoton Solar Reviews ya ce tun a shekarar 1979 lokacin mulkin shugaban ƙasa Jimmy Carter, aka saka allunan wutar sola guda 32 a saman rufin White House don dumama ruwa.
Duk da cewa waɗancan allunan ba su dade ba bayan mulkin Carter, a shekarar 2017 ya sanya allunan wutar sola kimamin 4,000 a gonarsa da ke Georgia.

Asali: Getty Images
A lokacin da ya samar da wutar sola gonar shi, Jimmy Carter ya samar da wutar da ke isar rabin bukatun mutanen garin Plains.
A yanzu haka dai wasu ‘yan ƙasa na yaba wa ƙoƙarin gwamnati na rungumar wutar sola, yayin da wasu ke bayyana damuwa kan kudin da za a kashe wajen aikin.
Nijar ta rungumi aiki da wutar sola
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta rage adadin wutar lantarki da take mikawa kasar Nijar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya biyo bayan sabanin da aka samu da kasar Nijar ne kan ficewa daga ECOWAS.
Biyo bayan matakin da Najeriya ta dauka, rahotanni sun nuna cewa kasar Nijar ta rungumi aiki da sola domin cike gibin da lamarin ya haifar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng