Ma'aikatan Gwamnati Sun Tsunduma Yajin Aiki, An Rufe Ofisoshin NiMet a Najeriya
- Ma’aikatan NiMet sun fara yajin aiki a fadin ƙasar nan, inda suke zagaye filayen jiragen sama don tabbatar da cewa an bi umarnin
- Ma’aikata sun koka da karancin albashi, suka ce wasu suna karɓar rance don biyan kuɗin haya da kudin makarantun 'ya'yansu
- Yayin da Paul Ogohi ya ce ma'aikatan NiMet na mutuwa kamar kaji, ya ce 70% na fama da hawan jini, 90% na da matsalolin ido
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ma’aikatan hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) sun fara yajin aikin gargadi a ranar Laraba, suka dakatar da duk wasu ayyuka a fadin ƙasa.
An lura cewa yajin aikin ya fara ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe, ma’aikatan NiMet da ‘ya’yan ƙungiyar suka riƙa zagaye filayen jiragen sama don tabbatar da umarnin.

Asali: Twitter
Ma'aikatan NiMet sun koka kan karancin albashi
Jaridar The Cable ta gano cewa wasu daga cikin ma’aikatan sun kwana a harabar ofisoshin hukumar domin tabbatar da cewa an dakatar da ayyuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani daga cikin ma’aikatan ya koka da cewa:
“Matsalolin da muke fuskanta a NiMet sun yi yawa. Albashi da duk wani alawus da muke samu sun yi kadan sosai idan aka kwatanta da wasu hukumomin gwamnati.
“Misali, wani ma’aikacin gudanarwa a NiMet na karɓar albashin ₦470,000, amma za ka samu a wata hukumar ana biyansa kusan ₦1.2m.
“Ko gwamnati ta yi karin albashi, mu ba mu samu. Muna gudanar da aiki mai muhimmanci fiye da sauran hukumomi, amma ta kai ko kudin haya, zirga-zirga, da kudin makarantar 'ya'yanmu ba ma iya."
Karin Matsalolin da ma'aikatan NiMet ke fuskanta
Jaridar Punch ta ma'aikacin da ya nemi a sakaya sunansa, ya kara da cewa:
“Yanayin aikin da muke yi ya yi tsanani. Muna buƙatar a kula da mu kamar yadda ake kula da sauran ma'aikatan wasu hukumomin.
"Ba wai wasu kudade masu yawa muke nema ba, kawai dai a rika biyanmu albashi mai kyau wanda zai ba mu kwanciyar hankali yayin gudanar da aiki.”
“Aikinmu ya shafi kula da yanayi a kan noma, ruwan sama da na sufuri ga fannoni daban-daban. Amma duk da haka, alawus ɗinmu ba zai iya biya mana buƙatu ba."

Asali: Twitter
"Ma'aikatan NiMet na mutuwa kamar kaji" - Kungiya
Sakataren hadakar kungiyoyin ma'aikatan hukumomin gwamnati, CSTRSE, Paul Ogohi, ya soki yadda wasu kamfanonin jiragen Najeriya ke aiki ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya sa ma'aikatan NiMet ke shan wahala.
"Ma'aikaran hukumar NiMet na ci gaba da mutuwa kamar ana yanka kaji. Kusan 70% na ma’aikatan hasashen yanayi na fama da hawan jini.
“90% ba sa gani sosai saboda yawan aiki wajen lura da sararin samaniya don sufurin jiragen sama. Muna da matsalolin ido.
“Muna roƙon Minista da ya taimaka mana. Muna ganin wasu sauye-sauye a wasu bangarori, amma ya kamata a fadada su zuwa NiMet saboda muna cikin mauyacin hali.”
- Paul Ogohi.
Malamai sun yi yajin aiki a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman firamare a Abuja sun sake shiga yajin aiki, lamarin da ya hana ɗalibai zana jarabawa kamar yadda aka tsara.
Malaman sun zargi shugabannin ƙananan hukumomi shida da gaza biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 duk da alkawarin da suka ɗauka a baya.
Sun bukaci a biya musu hakkokinsu cikin gaggawa domin su koma bakin aiki, tare da nuna damuwa kan tasirin hakan ga ci gaban ilimi a babban birnin ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng