Bayan Shekara da Rasuwa, za a Yi Taron Tunawa da Buhari na Farko a Najeriya
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya kusa cika shekara daya da rasuwa bayan jinyar da ya yi a birnin London
- Biyo bayan haka, 'yan uwa da abokan arziki sun shirya wani taro na musamman domin tunawa da tsohon shugaban kasar
- Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan kammala mulkin Najeriya na shekara takwas da ya yi tsakanin 2015 zuwa 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masoya da sauran 'yan uwan marigayi shugaba Muhammadu Buhari za su yi wani taro a Abuja domin yi masa addu'o'i.
Za a yi taron ne a watan Yuli mai kamawa, wanda zai dace da ranar da tsohon shugaban kasar ya kwanta dama a wani asibiti a London.

Source: Facebook
Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ne ya wallafa sako game da taron da za a yi domin tunawa da marigayin a shafinsa na Facebook.
Za a yi ton tunawa da Buhari
A sanarwar da Bashir Ahmad ya fitar, ya bayyana cewa za a yi taron ne kawai domin tunawa da abubuwan da Buhari ya yi na cigaban kasa da za su sanya a yi masa addu'o'i.
Tsohon hadimin Buhari ya ce:
"Za a gudanar da taro a Abuja ranar Litinin, 13 ga Yulin 2026, domin yi wa tsohon shugabanmu, shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga Yuli, 2025, addu'a tare da girmama shi.
"Allah Ya haskaka kabarin Baba."
Martanin 'yan Najeriya
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi game ada sanarwar da Bashir Ahmad ya fitar a kan taron tunawa da Muhammadu Buhari.
Amb. Aniefiok Jimmy ya ce:
"Allah Ya jiƙan Baba. Ka huta lafiya, Janar — Ba za a manta da hidimar da ka yi wa Najeriya ba.
Bashir Ahmad, ina roƙon ka da ka ba ni ɗan lokaci domin in bayyana wani shiri da na tsara wanda zai taimaka wajen ci gaba da raya tarihin Shugaba Buhari ta hannun Yusuf Buhari."

Kara karanta wannan
'Dan majalisar Amurka ya fadi kokarin da ya yi don kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya
Zuwairiyyah Adamu Girei ta ce:
"Allah Ya ci gaba da ba shi hutu na har abada. Amin."
Mu'azu Galadima ya ce:
"Allah Ya yi masa rahama, Ya ba shi gidan Aljanna. Amin Ya Allah. Tasirin da Baba Buhari ya yi zai ci gaba da kasancewa har abada."
Buhari Ibrahim ya ce:
"Ubangijin Al'arshi Mai Girma Ya ƙara masa rahama. Amin."

Source: Instagram
Kabiru Muhammad ya ce:
"Allah Ya jiƙan Baba Buharinmu mai gaskiya da rahama."
Kaka Mai Bukar Kauwa ya ce:
"Don Allah ku ƙyale wannan mutum ya huta mana!"
Muhammad Alh Umar ya ce:
"Amin Ya Allah. Da a ce ina da hali da ni ma zan halarta. Amma duk da haka, In Sha Allah zan yi tawa addu'ar. Allah Ya haskaka makwancin Baba.
"Wallahi ni masoyin Baba ne na gaskiya, har wasu daga cikin abokaina suna yawan magana a kan wannan ra'ayin nawa."
Yusuf Buhari ya shiga siyasa
A wani labarin mun kawo muku cewa dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan.
Yusuf Buhari ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin kawo cigaba ga mutane tare da jaddada wa al'umma cewa zai rike amana.
A yanzu haka Yusuf Buhari ya samu tikitin takarar majalisar wakilai a karkashin jam'iyayar APC domin fafatawa a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

