Shekaru da Barin CBN, Sanusi II Ya Fayyace Hakikanin Alakarsa da Yar’adua da Jonathan

Shekaru da Barin CBN, Sanusi II Ya Fayyace Hakikanin Alakarsa da Yar’adua da Jonathan

  • Muhammadu Sanusi II ya yi wa ma’aikata bayanin yadda za su zauna da shugabanninsu salin-alin ba tare da shiga matsala ba
  • Sarkin Kano ya kawo misalign yadda ya shawo kan Goodluck Jonathan sa’ilin da ya nemi a rage ruwan da ke cikin bashin banki
  • Tsohon gwamnan na CBN ya tuno wani zama da ya yi da Ngozi Okonjo Iweala yayin da ta ke Ministar tattalin arzikin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da alakarsa da shugabannin kasar da ya yi aiki da su a lokacin yana gwamnan CBN.

Marigayi Ummaru Musa Yar’adua ya nada Muhammadu Sanusi II a matsayin gwamnan babban banki, amma ya rasu ya bar shi a kujerar.

Sanusi II da Jonathan
Muhammadu Sanusi II lokacin yana CBN da Goodluck Jonathan wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Muhammadu Sanusi II ya yabi Yar'adua & Jonathan

A wani bidiyo da aka gani yana yawo a Shafin TV Platinum a Facebook, Muhammadu Sanusi II ya yabi masu gidansa lokacin da yake ofis.

Kara karanta wannan

Bayan shekara da rasuwa, za a yi taron tunawa da Buhari na farko a Najeriya

Duk da Goodluck Jonathan ya yi sanadiyyar barinsa CBN a 2013, an ji masanin tattalin arzikin yana yabon gwamnatinsa da Ministan kudi ta lokacin.

“Na yi aiki da shugaba Yar’adua da Jonathan, kuma maganar gaskiya a shekarun da na yi a CBN, babu wanda ya nemi ya matsa mani a aiki na.
"Eh, sukan samu matsala, wani lokaci sukan yi mani magana kuma in yi masu bayani, amma ba su taba tursasa mani a game da manufofin kudi ba."

Yadda Sanusi II ya gamsar da shugaba Jonathan

Muhammadu Sanusi II ya tuno wani zama da ya yi da Goodluck Jonathan lokacin da aka koka cewa ruwan da ke kan bashin banki ya yi yawa.

Sarkin Kano yake cewa ya yi wa Jonathan bayani cewa idan aka rage ruwa, wasu tsirarrun kamfanoni za su samu kudi cikin sauki daga hannun bankuna.

Amma ba a nan gizo ke sakar ba, Sanusi II ya ce sai ya fada wa Jonathan cewa muddin aka yi hakan, farashin kaya za su tashi a kasuwa.

A karshe dai sai dai Jonathan ya hakura da shi da ya fahimci gamsassun hujjojin da ya ba shi na tashin kaya da za a gani a kasuwanni.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ndume ya gano matsalar da Tinubu ke fuskanta a fadar shugaban kasa

“Kai! Ku masana tattalin arzikin nan...”
Sanusi II
Tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi II da Ngozi Okonjo Iweala tare da Christine Lagarde a wani zama Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maimakon ya buga kudi, gwamnan CBN ya ki yarda a bari a yi sanadiyyar tashin Dala a kan Naira. Jaridar Sahara Reporters ta kawo labarin ranar Juma'a.

Khalifan na Tijjaniya ya bada wannan labari ne wajen taron NILDS ne domin nuna wa manyan ma’aikata yadda za su shawo kan manyan su a wajen aiki.

Wata haduwar Sanusi II da Okonjo-Iweala

Fai-fan bidiyon yana dauke da bayanin yadda Sanusi II ya ki amincewa da bukatar Ngozi Okonjo Iweala na ba Gwamnatin Najeriya bashi.

Sanusi ya ki yarda ya karya doka domin gwamnati ta samu aron kudi daga hannun CBN kuma ya ce ministar tattalin arzikin ta fahimce shi da kyau.

Sauke Sanusi II daga CBN

A wani rahoto, an ji tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana a wani taro a Abuja inda ya bayyana dalilin da ya sa ya dakatar da Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Jonathan ya ce bayanin da Sanusi ya bayar kan dalilin sauke shi ba daidai ba ne, ya ce ba zargin batan $49.8bn ba ne ya sa ya dakatar da shi, sai dai don wani korafi.

Basaraken ya saba cewa aikin da ke gaban sa a lokacin shi ne fitar da manufofi da tsare-tsaren kudi, da kula da bankuna ba biye wa gwamnatin tarayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng